Kwankwaso Ya Yi Gini a Kan Ruwa, Jagoran Kamfe da Mutanensa Sun Watse Daga NNPP
- Kwanan nan Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya babban gangamin NNPP na Arewa maso gabas
- Ba a dade ba sai ga shugaban yakin neman takarar jam’iyyar NNPP na yankin, ya sauya-sheka
- Babayo Liman ya bada sanarwar shiga PDP, ya ce shi da mutanensa za su bi bayan Atiku Abubakar
Bauchi - Kwanaki kadan bayan Rabiu Musa Kwankwaso mai neman shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya ziyarci jihar Bauchi, mutanensa sun sauya-sheka.
Daily Trust ta ce babban shugaban yakin neman zaben jam’iyyar adawa ta NNPP a Arewa maso gabas, Dr. Babayo Liman ya sauya-sheka a cikin makon nan.
Dr Babayo Liman da daruruwan mabiyansa sun koma PDP wanda it ace babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, za su zabi Alhaji Atiku Abubakar a 2023.
Liman da magoya bayansa sun rabu da Rabiu Kwankwaso, sun koma goyon bayan Atiku kamar yadda suka bayyana a sakatariyar kungiyar NUJ da ke Bauchi.
Atiku ne mafita a 2023 - Liman
Tsohon shugaban yakin neman takaran NNPP a jihohin na Arewa maso gabashin Najeriya ya ce sun gamsu ‘dan takaran PDP ne zai iya shawo kan kasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
La’akari da cewa Atiku Abubakar ya yi shekaru takwas a kan kujerar mataimakin shugaban kasa, ya san hanyar da za a bi wajen ceto tattalin arzikin Najeriya.
Dr. Liman ya ce daga yanzu ya tashi daga matsayinsa na ‘dan jam’iyyar NNPP kuma mabiyin Kwankwasiyya, ya ce shi da mutanensa sun canza sheka.
Ina sanar da ku na bar Jam'iyya
“Na zo sakatariyar NUJ na reshen jihar Bauchi domin in sanar da manema labarai da sauran jama’a cewa a yau, ni Babayo Liman na ajiye mukamai na.
Na sauka daga kujerar Sakataren yankin Arewa maso gabas, ‘dan kwamitin yakin zaben shugaban kasa, jagoran Kwankwasiyya kuma ‘da a jam’iyya.
Na zo tare da shugabannina da dubunnan magoya baya domin mu shaida niyyarmu na shiga PDP domin goyon bayan Atiku Abubakar da Bala Mohammed.”
- Babayo Liman
New Telegraph ta ce Liman ya yi kira ga mutanensa da ke Arewa maso gabas su bar NNPP.
Ana tsere kan kuri'un Kano
Kun ji labarin yadda Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka kwallafa rai a kan miliyoyin kuri’un da za su fito a Jihar Kano a 2023.
‘Yan Takaran kujerar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyun APC, PDP, NNPP da LP sun fito da dabarun da za su cece su kan abokan gaban a zaben bana.
Asali: Legit.ng