Ku Hada Kai Ku Zabi Shugabanni Nagari, Sheikh Gumi Ga Musulman Najeriya

Ku Hada Kai Ku Zabi Shugabanni Nagari, Sheikh Gumi Ga Musulman Najeriya

  • Sheikh Ahmad Gumi ya roki daukacin al'ummar Musulmai su hada kansu domin umarni ne na Allah matukar suna son cin nasara
  • Shehin Malamin wanda ya yi fice mazaunin Kaduna ya jero abinda ya kamata Musulmai su duba kafin zaben shugabanni
  • Sheikh Gumi da Sarkin Zazzau sun yi wa Musulmai Nasiha kan falalar gina Masallaci dakin Allah

Kaduna - Shahararren Malamin addinin Islama na Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya roki Musulmai su hada kai su zabi mutanen da suka dace masu tsoron Allah a zabe mai zuwa.

Sheikh Gumi ya yi wannan roko ne a wurin kaddamar kaddamar da asusun fadada Masallacin Dan Fodiyo da ke jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi.
Ku Hada Kai Ku Zabi Shugabanni Nagari, Sheikh Gumi Ga Musulman Najeriya Hoto: Sheikh Ahmad Gumi
Asali: Twitter

Fitaccen Malamin ya roki Musulmai su guji duk wani aiki da zai kawo rabuwar kai a tsakaninsu kuma su maida hankali wajen zaman lafiya a arewa da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC Sun Damke Mai POS da 'Yan Bindiga Suka Girke Yana Musu Hada-hadar Kudi

A cewar Sheikh Ahmad Gumi, hadin kan Musulmi umarni ne na Allah SWT matukar suna son kasancewa da karfi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"Shugabanci kamar tabarma ce wacce ba da jimawa ba zaka ga an nannaɗe ta. Hadin kanmu shi ne karfinmu kuma mu sani umarni ne na Allah Musulmai su hada kai su so junansu matukar suna son nasara."

Wane dan takara ya kamata Musulmai su zaba?

Malamin ya ci gaba da cewa:

"Wajibi mu zabi shugaba mai sauraron koken talakawansa, wajibi mu zabi shugaba mai tsoron Allah kuma jagora mai girmama Addinin mu. Idan har muka yi haka to mu barwa Allah sauran."

Sheikh Gumi ya jaddada bukatar Musulmai su zuba jarinsu wajen gina Masallaci, inda ya bayyana cewa faɗaɗa dakin Allah sunnah ce ta Manzon Allah SAW.

A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli, wanda ya samu wakilcin wazirinsa, Khadi Muhammad Inuwa Aminu, ya roki Musulmai su ba da gudummuwar sake gina Masallacin.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

A cewarsa, gudummuwa domin gina Masallaci ɗakin Allah zai sa su samu lada mai dumbin yawa.

Kar Ku Zabi Yan Siyasan Da Zasu Murkushe Yan Ta'adda, Sheikh Gumi

A wani labarin kuma Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci yan arewa karsu zabi maau cewa zasu halaka yan fashin daji idan suka ci zabe

Shehin Malamin yace arewa ba ta bukatar wanda zai kawo karshen yan bindiga, tana son wanda zai sulhu ya masu abinda suke bukata.

Sheikh Gumi ya jima tsawon shekaru yana kira da a yi sulhu da 'yan bindiga, waɗanda suka jefa mutane da yawa cikin matsin rayuwa ta hanyoyi da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262