Jam'iyyar LP Ce Babban Kalubalen Mu a Shiyyar Kudu Maso Gabas, Bukola Saraki

Jam'iyyar LP Ce Babban Kalubalen Mu a Shiyyar Kudu Maso Gabas, Bukola Saraki

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yace babu tantama PDP zata lashe kuri'un shiyyoyi hudu a zabe mai zuwa
  • Saraki ya bayyana cewa PDP na da babban kalubale a shiyya biyu, kudu maso gabas da kudu maso yamma
  • Tsohon gwamnan jihar Kwara na daya daga cikin 'yan takarar da suka sha kaye a zaben fidda gwanin PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Buƙola Saraki, yace jam'iyar Peter Obi (LP) ce babban kalubalen PDP a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Saraki ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da gidan Talabijin din Arise Tv cikin shirin Morning Show ranar Litinin 16 ga watan Janairu, 2023.

Atiku da Bukola Saraki.
Jam'iyyar LP Ce Babban Kalubalen Mu a Shiyyar Kudu Maso Gabas, Bukola Saraki Hoto: Bukola Saraki
Asali: UGC

Saraki ya ce:

"Kudu maso kudiu yanki ne da PDP ke da karfi, zamu tabuka abinda ya dace a kudu maso kudu, kudu maso gabas kuma babban kalubalen mu a shiyyar ita ce Laboura Party."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya Ja Kunnen Ganduje Kan yi Masa Zagon Kasa a Zaben 2023, Yace Zai Tafka Nadama

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Amma duk da haka zamu yi abin da ya dace a Kudu maso gabas, zamu samu kaso 25% da ake bukata. Zamu yi abu mai kyau a shiyyar araewa ta tsakiya, haka nan mu ke da arewa maso yamma da arewa maso gabas."

Atiku zai samu nasara a shiyyoyi hudu cikin Shida - Saraki

Jaridar Leadership ta rahoto Bukola Saraki na cewa jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, zasu lashe mafi yawan kuri'u a shiyyoyin Najeriya huɗu.

Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara yace PDP zata samu galaba da shiyyoyin Arewa maso yamma, arewa maso gabas, arewa ta tsakiya da kudu maso kudu a zabe mai zuwa.

"Shiyya hudu da zamu samu galaba sun hada da, arewa maso yamma, arewa maso gabas, kudu maso kudu da arewa ta tsakiya kuma zamu samu kaso 25% a jihohi sama da 24, babu tantama a kan haka."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Gamu Da Taskun Matasan Yankinsa, Inda Suka Zargeshi Da Yin Watsi Da Su

"Muna bukatar shiyyoyi hudu ne kawai, da zaran mun samu nasara a shiyya hudu to mun ci zabe."

Wane shiyyoyin ne PDP ba zata kai labari ba?

A cewar Bukola Saraki, Labour Party ce kadai zata kawo cikas ga PDP a shiyyar kudu maso gabas yayin da APC mai mulki zata mamaye kudu maso yammacin Najeriya.

A wani labarin kuma dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ya tsira daga wasu dandazon mutane da suka so mamaye shi a Enugu

Mai tuka jirgin Helkwaftan da dan takarar zai shiga ne ya yi hanzarin janye Obi ya tura shi cikin jirgi bayan kammala taro a jami'ar Nsukka.

Yan Najeriya sun maida martani kan Bidiyon da ya nuna yadda matukin jirgin ya ceci Obi, wasu na ganin dan takarar ya cinye kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262