Jam'iyyar APC Ta Karvi Dubbannin Masu Sauya Sheka Daga PDP, NNPP a Neja
- Kwanaki 40 gabanin babban zabe, jam'iyya mai mulki ta samu karin goyon baya a shiyyar arewa ta tsakiya
- Manyan jiga-jigai da shugabannin PDP, mambobin NNPP da wasu jam'iyyu sun sauya sheka zuwa APC a jihar Neja
- Dan takarar gwamnan Neja a APC ya ce idan ya kai ga nasara a watan Maris, mutanen Neja zasu amfana da gwamnatinsa
Niger - Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar arewa ta tsakiya, Alhaji Mu’azu Bawa, ya karbi masu sauya sheka 4,780 daga jam'iyyun siyasa daban-daban.
Leadership ta tattaro cewa an samu wannan ci gaban a wurin gangamin fara kamfen a mazabar Sanatan Neja ta arewa wanda ya gudana a Kontagora, hedkwatar APC ta shiyya.
Yace masu sauya shekan sun kunshi shugabannin jam'iyyar PDP 87, da kuma mata 261, sai kuma maza jiga-jigai daga jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Alhaji Bawa ya kara da cewa APC a shirye take ta samar wa kowane cikakken ɗan ƙasa damar baje basirarsa domin cika burinsa na siyasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Zan dora daga inda magabaci na ya tsaya - Bago
A bangarensa, dan takarar gwamnan jihar Neja a inuwar APC, Umar Mohammed Bago, ya tabbatar da cewa idan ya kai ga nasara zai karisa dukka ayyukan da gwamnati mai ci ta fara.
Da yake jawabi ga dandazon magoya baya a karamin filin wasan Kontagora, dan takarar ya baiwa jama'ar Neja tabbacin cewa duk alkawurran da ya ɗauka a kamfe zai cika su idan har suka zabe shi.
Ya kara da cewa gwamnatinsa zata dora daga inda wanda ya gada ya tsaya wajen samarwa al'umma mahalli mai kyau da walwala.
Bugu da kari, Mista Bago yace gwamnatinsa zata maida hankali sosai wajen rage zaman kashe wandon matasa ta hanyar sama masu jari da kuma ilimi mai inganci.
A cewarsa zai inganta rayuwar matasan jihar ta yadda zasu zama masu ba da gudummuwa wurin ci gaban Neja, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A wani labarin kuma Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023
Mai taimaka wa gwamna Ugwuayi na jihar Enugu a bangaren midiya, Emmanuel Jonathan yace ba zai cigaba da rufa-rufa ba, ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi.
Hadimin gwamnan, daya daga cikin mambobin G5 na PDP, yace ba zai tsaya yana gani wasu na jan ragamar kasar nan da son rai ba .lokaci ya yi da za'a ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng