Zan Yi Amafani da Tsarin Musulunci Idan Na Ci Zaben 2023, Dan Takarar Gwamnan Katsina
- Dan takarar gwamnan Katsina na NNPP ya sha alwashin komawa tafarkin Musulunci idan ya ci zaben 2023
- A wurin taron bayyana manufofin yan takara da aka shirya, dan takarar yace Musulunci ne kadai mafita daga matsaloli
- Midiya Trust tare da hadin guiwar Cibiyar habaka Demokuradiyya da wasu kafafen watsa labarai ne suka shirya taron
Katsina - Dan takarar gwamnan Katsina na New Nigerian People Party (NNPP) ya yi alkawarin kafa gwamnati bisa tsarin Musulunci a idan aka zabe shi a watan Maris.
Dan takarar ya dauki wannan alkawari ne a wurin taron al'umma na yan takarar gwamnan jihar wanda Mediya Trust watau kamfanin jaridar Daily Trust ya shirya ranar Asabar.
Da yake jawabi a wurin, Dakta Rabe Darma, dan takarar mataimakin gwamna wanda ya wakilci jam'iyyarsa yace idan ya tabbatar da tsarin gwamnatin Musulunci a karshen 2023, cin hanci da rashawa ya kare a Katsina.
Da Gaske ICPC Ta Kama Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Kan Badakalar Biliyan N12? Aliyu Sokoto Ya Fayyace Gaskiyar Lamari
Yayin da yake sukar gwamnatin APC mai mulki a jihar, ya yi alkawarin lalubo wasu hanyoyin samun kuɗin shiga, wadan da zasu sa jihar ta daina dogaro da kasafin tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Darma ya ce:
"Zamu koma tsarin tafiyar da gwamnatin Musulunci kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar mana a Addinin mu (Alkur'ani da Hadithi). Tsarin zai magance mana duk wata damuwa da muke fama da ita a kasar nan."
"Haka nan idan kuka duba mun rasa tsarin shugabanci mai kyau a jihar Katsina, saboda zamu koma tsarin ta yadda kasafin da za'a turo mana zai zama ƙaso 20% ne kacal na kudin shigarmu."
Legit.ng Hausa ta gano cewa Midiya Trust ce ta jagoranci shirya taron tare da tallafin cibiyar raya Demokuradiyya (CDD).
Sauraran kafafen watsa labarai da suka ba da hadin kai wajen shirya zaman sun hada da, Vision FM, Farin Wata TV da kuma Katsina City News wacce ke tafiyar da harkokinta a yanar gizo.
Legit.ng Hausa ta tattauna da wasu mazauna Katsina kan wannan batu dan takarar NNPP, an samu ra'ayoyi mabanbanta.
Mustapha Ahmad, wani dan kasuwa a karamar hukumar Ɗanja, yace maganar ɗan takarar NNPP tana kan hanya domin muslunci na da maganin komai.
"Maganarsa gaskiya ce, akwai maganin komai a Musulunci amma matsalar alkawarin yan siyasa, su gama dadin baki a Kamfe da sun ci zabe mu ji shiru," inji shi.
Haka nan Malam Abubakar da aka fi da Balarabe ya bayyana wa wakilin mu cewa shi bai ji maganarba da kunnensa amma idan ya tabbatar to kuri'arsa ta NNPP ce.
Murtala Ahmad Mani dake jihar Katsina ya gaya wakilin mu cewa duk wani kamfen yan siyasa jinshi kawai suke, "A ranar zabe zamu tantance wa ke da niyga mai kyau mu zabe shi.
APC da PDP sun kashe kasa - Kwankwaso
A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Fara Kamfe Gadan-Dagan, Ya Ce APC da PDP Sun Kashe Kasa
Kwankwaso ya fara kamfen neman zama shugaban kasa a Bauchi, ya shawarci yan Najeriya su kaucewa duk wata jam'iyya su zabi NNPP.
Tsohon gwamnan Kano ya ce tsawon shekaru 24, APC da PDP na juya akalar kasar nan amma ba abinda suka tsinana sai tulin matsala, yace NNPP ce mafita.
Asali: Legit.ng