Ana Daf da Zabe, Hukuncin Kotu ya Kuma Canzawa Jam’iyyar APC ‘Dan Takarar Sanata
- Kotu ta canza wanda zai yi wa jam’iyyar APC takarar kujerar Sanata a mazabar Kudancin jihar Bauchi
- Alkalan kotun daukaka kara sun ba Shehu Umar gaskiya cewa shi ne wanda ya lashe zaben tsaida gwani
- A hukuncin da aka rika yi a baya, Ibrahim Zailani ne aka tabbatar a matsayin ‘dan takaran Sanatan yankin
Abuja - Premium Times ta ce kotun daukaka kara da ke garin Abuja, ta dawowa Shehu Umar da tikiti, ta tabbatar da shi a matsayin ‘dan takara.
A ranar Juma’a, 14 ga watan Junairu 2023, kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa Shehu Umar zai yi wa APC takarar Sanatan Kudancin jihar Bauchi.
Kafin yanzu, Emeka Nwite da wasu Alkalan babban kotun tarayya sun soke takarar majalisar dattawan da Shehu yake yi a karkashin jam’iyyar APC.
A hukuncin da ya zartar dazu, Mai shari’a Ridwan Abdullahi ya ce kotun bayansu tayi kuskure wajen karbe tikiti daga hannun ‘dan takaran Sanatan.
Ibrahim Zailani ya sha kashi
An yi gardamar takara ne tsakanin Shehu Umar da Ibrahim Zailani a shari’a mai lamba CA/ABJ/CV/1335/2022 a kotun daukaka karan na Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng Hausa ta fahimci sauran wadanda aka yi kararsu sun hada da APC da INEC.
Alkalai sun ba Jibrin Jibrin gaskiya
Lauyan wanda ya shigar da kara, Jibrin Jibrin ya gamsar da Alkali cewa babu dalilin soke zaben fitar da gwani da APC ta shirya a karshen Mayun 2022.
Alkalai biyu suka zartar da hukunci wanda ya daukaka karar ya yi nasara, hakan ya na nufin sun fahimci an tafka kuskure a hukuncin kotun tarayyar.
Da wannan hukunci da babban kotun na garin Abuja ta zartar, Umar Shehu zai tsayawa APC a takarar ‘dan majalisar dattawa na kudancin Bauchi.
Jaridar ta ce idan dayen bangaren bai gamsu da hukuncin da aka yi ba, zai iya zuwa kotun koli. A nan ne za a raba gardamar takarar kujerar siyasar.
PDP ta shiga uku a Imo
Emeka Ihedioha yana cikin wadanda ake ganin su na da kusanci da ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar, amma kun ji labari PCC bai yarda da shi ba.
Ihedioha baya ga matsayinsa tsohon Gwamna, ya rike mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya a lokacin Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Legit.ng