2023: Bayan Murabus Din Okupe, Jam'iyyar Labour Ta Kori Ciyaman Dinta A Wata Muhimmiyar Jiha, Obi Ya Tabu
- An cire shugaban jam'iyyar Labour ma jihar Bayelsa, Eneyi Zidougha, daga ofishinsa a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu
- Majiyoyi kwararara sun bayyana cewa an cire Zidougha ne ta hanyar kada kuri'ar rashin amincewa yayin babban taron jihar a Yenagoa
- An tattaro cewa an maye gurbin Zidougha da Ebi Sikpi, bayan zarginsa da bannatar da kudade da rashin biyayya ga jam'iyyar
Yenagoa, Bayelsa - Jam'iyyar Labour, LP, ta jihar Bayelsa ta kori ciyaman dinta, Eneyi Zidough kan zargin almubazaranci da kudi, cin amanar jam'iyya da hure wa yan takara kunne gabanin zaben 2023.
Punch ta rahoto cewa masu ruwa da tsaki a LP sun cire Zidougha daga ofis ta hanyar kuri'ar rashin amincewa yayin babban taron jihar da aka yi a sakatariyarta a Yenagoa a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wurin taron, an maye gurbin ciyaman din da aka cire da tsohon mataimakin ciyaman na LP a Bayelsa Central, Ebi Sikpi.
A cewar mataimakin sakataren LP, Theophilus Taribo, an yi taron kan ka'ida kuma cire Zidougha da aka yi bisa dokokin jam'iyyar ne.
Taribo ya ce:
"An bi dokokin da ke cikin kundin tsarin mulki; wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin jam'iyya na jiha, mambobi na kananan hukumomi. An kira taron bisa kundin tsarin jam'iyyar."
Sikpi ya yi magana kan yi wa Peter Obi aiki
A bangarensa, Sikpi ya sha alwashin yin aiki tukuru tare da shugabannin jam'iyyar, masu ruwa da tsaki da magoya baya don nasarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, da saura da ke takarar a jam'iyyar LP.
"Za mu tabbatar an hada kan jam'iyyar saboda zaben mai gidan mu, Peter Obi. Muna fatan nasara, haske ya zo jam'iyyar mu a jihar Bayelsa."
Yar Takarar Kujerar Mataimakiyar Gwamna Ta Sauya Sheka Daga APC zuwa PDP
A wani rahoton, Misis Helen Boco, tsohuwar yar takarar kujerar mataimakiyar gwamnan a zaben shekarar 2019 a jihar Cross Rivers a APC ta koma jam'iyyar PDP.
A cewar wani rahoto da Tribune ta wallafa, Boco ta sauya shekar ne yayin da ya rage kwana 49 a yi babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023.
Asali: Legit.ng