Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

  • Manyan ‘yan takaran kujerar shugabancin Najeriya za su gwabza wajen samun kaso mai tsoka daga kuri’u miliyan 5.9 da ake da su a jihar Kano
  • Mutane kusan miliyan shida suke da katin zabe a jihar Arewacin Najeriyar, kuma mutanen Kano da yawa su kan fito su kada kuri’arsu a lokacin zabe
  • A ranar Juma’a, 13 ga watan Junairu 2022, Daily Trust ta fitar da dogon rahoto a kan yadda jam’iyyun PC, PDP, NNPP da LP ke neman kuri’un jihar

Rahoton nan ya tattaro yadda kowane ‘dan takara da jam’iyyarsa suke neman galaba a zaben watan gobe.

1. APC

A Junairun nan ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya hada gagarumin taro a Kano wanda ya ba shi karfin gwiwar zai samu nasara a karkashin jam’iyyar APC.

Tinubu ya dogara da Gwamna Abdullahi Ganduje, da masu mukamai da kaunar da Kanawa suke yi wa Muhammadu Buhari, yana sa ran farin jinin ya shafe shi.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP Ta Fasa Kwai, Wanda Aka ba Takara Ya Yaudare ta Bayan Karbar N500m

Gwamnan Kano ya nemawa ‘dan takaran goyon baya malaman addinin musulunci, shi kuma Tinubu a bangarensa, ya ba mutanen Kano kula na musamman.

2. PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar ta ce Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a PDP ya dogara da irinsu Malam Ibrahim Shekarau wanda ya dauke daga jam’iyyar NNPP.

Wazirin Adamawa yana sa ran ‘yan PDP za su taimaka masa wajen yakar NNPP da ‘Yan Kwankwasiyya masu goyon bayan tsohon Gwamna, Rabiu Kwankwaso.

Takarar 2023
Bola Tinubu a Kano Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kwanakin baya ya ziyarci Kano kuma ya tare a jihar da nufin a watan gobe ya samu kuri’un da suka zarce 391,593 da samu a PDP a jihar a zaben shekarar 2019.

3. NNPP

Tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso yana sa ran mabiyansa da wadanda suka amfana da shi da gwamnatinsa za su taimaka masa wajen yin nasara.

Kara karanta wannan

PDP Ta Dauko Sabon Salo, Tana Kokarin Hada-Kai da Jam’iyyu 11 Domin Kifar da APC

‘Dan takaran na jam’iyyar NNPP yana sa ran zai tabuka abin kirki a zaben 2023 musamman a Kano. Kwankwaso yana tare da manyan ‘yan siyasa a NNPP.

Jaridar ta bi tarihi, ta kawo yadda Ibrahim Shekarau a lokacin yana Gwamna ya yi takarar shugaban kasa a ANPP, ya samu kuri’u 526,310, CPC ta samu 1.62m.

4. LP

Akalla sau biyu Peter Obi ya ziyarci Kano saboda neman kuri’un mutanen jihar. Masana su na ganin LP ta fi karfi a irinsu Sabon Gari inda ya tara mutanen waje.

Obi ya ziyarci Sarakunan Kano a wata ziyara da ya kawo da nufin samun karbuwa. Jam’iyyar ta dogara ne da irinsu Bashir I. Bashir mai yi mata takarar Gwamna.

NNPP tayi nasara a kotu

Rahoton da muka fitar a baya ya nuna Jam’iyyar NNPP ta maye gurbin Sanata Ibrahim Shekarau da wasu ‘Yan takara 80 da aka tsaida a tashin farko.

Shugaban NNPP, Farfesa Ahmed Rufai Alkali ya ce sun je kotu domin a tursasawa INEC karbar sababbin ‘yan takaransu bayan abubuwan da suka faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng