Lema Ta Yage a Gombe, Kakakin PDP Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar Su Kwankwaso
- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ci gaba da haduwa da manyan cikas kasa da makonni bakwai kafin babban zabe
- A jihar Gombe, jam’iyyar ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta inda ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)
- Murtala Usman Dukku, wanda ya rike mukamin kakakin jam’iyyar a Gombe ya bi sahun jiha-jigan jam’iyyar zuwa NNPP
Gombe- Kasa da kwanaki 45 kafin zaben 2023, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Gombe ta hadu da gagarumin cikas yayin da kakakinta, Murtala Usman Dukku ya yi murabus.
Wani rahoton Nigerian Tribune ya ce bayan yin murabus daga PDP, Dukku ya kowa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu.
PDP ta dakatar da Dukku kafin sauya shekarsa
Sai dai kuma, kafin murabus dinsa, an tattaro cewa PDP ta dakatar da Dukku kan zargin yiwa jam’iyyar zaton kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani ga dakatar da shin, Dukku ya gaggauta mika takardar murabus dinsa a wata wasika da ke bayyana ra’ayinsa na son barin jam’iyyar gabannin zaben 2023.
Dukku ya zama mamba na jam’iyyar NNPP a ranar Laraba, inda ya shiga jerin sunayen wadanda suka bar PDP da APC a jihar Gombe a yan makonnin da suka gabata.
Musa Gwani Bimason, babban jigon PDP wanda ya yi aiki a matsayin shugaban reshe na jam’iyyar a Gombe da mataimakinsa Yusuf Pindiga ma sun koka NNPP, rahoton The Sun.
Hakazalika mutane kamar su Hon. Rambi Ayala da Hon Hamza, yan majalisa masu wakiltan Billiri ta Gabas da Funakaye ta Kudu sun fice daga jam’iyyar.
Har ila yau, shugabar matan PDP, Maryam Muhammad Audi da Asabe Saleh suma sun shiga jerin jiga-jigan jam’iyyar da suka fice zuwa NNPP gabannin zaben 2023.
Sanatan APC ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotu na hana shi takara a zaben 2023
A wani labari na daban, Sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa a majalisar dokokin tarayya, Sanata Elisha Abbo ya yi martani a kan hukuncin babban kotun jihar da ta haramta masa yin takara a zabe mai zuwa.
Sanata Abbo ya ce zai garzaya kotun gaba domin daukaka kara a kan hukuncin.
Asali: Legit.ng