Dan Chinan Nan Da Ake Zargi Da Kashe Budurwasa Ummita Yace Ya Kashe Mata Kudi Kimanin N60M

Dan Chinan Nan Da Ake Zargi Da Kashe Budurwasa Ummita Yace Ya Kashe Mata Kudi Kimanin N60M

  • A shekarar data gabata ne aka samu wani dan kasar Sin da zargin kashe budurwarsa, kan cin amanarsa ko kuma yaudararsa
  • Tun a lokacin aka gurfanar dashi a gaban kotu, kuma kotu ta dage shari'ar har sai an samu tafintan da zai ringa fassara masa shari'a zuwa yarensa
  • A zaman kotun farko da aka fara gudanarwar dan China ya musanta zargin tare da nuna kazafi ake masa

Kano - Dan kasar sin din nan da ake zargi da kashe budurwarsa, Fran Geng Quarong yace ya kashewa budurwarsa kusan Naira miliyan 60 akan ita budurwarsa tasa a soyayyar da sukai a shekara biyu.

Quarong yayi wannan batun ne a babban kotun jihar mai zamanta a titin Miller wanda kuma mai shari'a Sunusi Ado Ma'aji yake jagoranta. Rahotan Daily Trust

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

Yace:

"Na siya mata gida wanda kudinsa yakai kusan N4m, da motar hawa wanda kudinta yakai N10m, kuma na bata kudin da akalla yakai N18m dan fara jari, kuma na siya mata jakankuna da sarkoki da ababen kwalliya wanda kudinsu sun kai N50,000 da kuma fara gina mata shagon da zata fara kasuwanci a Abuja"

Quarang ya ci gaba da cewa:

"Bayan makudan kudaden da na kashe mata, na sha daukarta na kaita wajajen siyar da abinci wajajen shakatawa da dai sauaransu"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan dan China yace ya siya mata gwala-gwalai da kudinsu yakai kusan N5m, sannan kuma na bata wasu kudaden masu yawa dan ta karbo shedar karatunta a jami'ar Sokoto.

Quarong yace:

Dan China
Dan Chinan Nan Da Ake Zargi Da Kashe Budurwasa Ummita Yace Ya Kashe Mata Kudi Kimanin N60M Hoto: Sahelian Times
Asali: UGC

Sun fara shirye-shiryen fara bikin aurensu, wanda hakan yasa ta nemi kusan N1.5m dan siyan kayan biki da kuma hada lefanta, da kuma neman karin wasu N700,000 dan yin liqi a wajen bikin

Kara karanta wannan

Rudani: DSS ta Gargadi 'Yan Najeriya, Ta Ce Akwai Munanan Abubuwan Da Za Su Faru Bayan Zaben Gwamnoni

Ba a iya nan kudin ya tsaya ba

Jaridar Sahelian Times ta rawaito cewa dan kasar Sin din yace ya kashe mata kudi kusan N700,000 lokacin da yaje ganin danginta a jihar Sokoto.

"A ranar 13 ga watan Satumban shekarar bara ta nemi na bata wasu kudade dan kammala ginin da ta ke yi a Abuja, amma ban bata ba sabida bani da kudi"
"To tun daga nan ne ta daina amsa kirana, sabida ta ga bani da kudi"

Yace bayan da tai aure kuma ta ci gaba da kiransa da kuma neman kudi a wajensa, yace akwai lokacin da ta zo kano tace allan fafur sai sun hadu.

Shedar mahaifiyar Ummita

Yayin da ta ke bada sheda kan abinda ya faru, mahaifiyar ummita tace ta ga raunuka kusan 11 a jikin marigayiyar yayin da ta je kan gawarta.

Rundunar yan sandan ta ce bincikenta ya gano wukar da akai amfani da ita wajen kashe marigayiyar lokacin da rashen rundunar na Dorayi ke bincike

Kara karanta wannan

An Kama Wani Mai Gida Bayan Ya Kai Sunayen Masu Haya Gidansa Shaharariyar Matsafa Bayan Sun Samu Saɓani

Mai shari'a Sunusi Ado Ma'aji, yace ya dage wannan karar zuwa yau din nan dan ci gaba da sauraran shedu.

Zamu ci gaba da kawo muku yadda shari'ar take gudana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel