Buhari Ya Zauna da Fastoci a Aso Villa, Ya Fada Masu Gaskiyar Batun Ɗaga Zabe

Buhari Ya Zauna da Fastoci a Aso Villa, Ya Fada Masu Gaskiyar Batun Ɗaga Zabe

  • Muhammadu Buhari ya yi zama da manyan fastoci a inuwar kungiyarsu ta CBCN a fadar Aso Rock
  • Shugaban CBCN na Najeriya, Rabaren Lucius Iwejuru Ugorji ya nemi alfarma a game da zaben 2023
  • Buhari ya tabbatarwa Lucius Ugorji da ‘yan tawagarsa cewa INEC ba za ta canza lokacin zabe ba

Abuja - A ranar Laraba, 11 ga watan Junairu 2023, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa mutanen Najeriya cewa babu maganar dakatar da zaben bana.

Daily Trust ta ce Shugaban Najeriyan ya bada wannan tabbaci ne a yayin da ya karbi bakuncin wasu fastoci a karkashin kungiyarsu ta CBCN a Abuja.

Da yake bayani a fadar shugaban kasa na Aso Villa, Mai girma Muhammadu Buhari ya fadawa malaman cewa za a shirya zabe a lokacin da aka tsara.

Wani wanda yana cikin tawagar da ta halarci zaman ya fadawa jaridar cewa shugaban kasa ya nuna ba a isa a canza ranar da za ayi zabe ba.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

Abin da aka samu daga wata majiya

“Shugaban kasan ya ce ranakun da Hukumar INEC ta ware na shirya babban zabe ba za su canza ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan yana kira ga kowa ya goyi bayan INEC wajen ganin ta shirya zabe mai nagarta, inganci da adalci.”

- Majiya

Buhari da Fastoci
Shugaba Buhari tare da Shugabannin CBCN Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Magana ta kare daga yanzu

Wannan ne karon farko da aka ji magana kai-tsaye daga bakin shugaban Najeriyan tun bayan da aka fara yawo da jita-jita cewa za a daga zaben bana.

Shugaban CBCN, Rabaren Lucius Iwejuru Ugorji da ya jagoranci tawagar, ya yabi shugaban Najeriya a kan irin gyare-gyaren da ya kawo a harkar zabe.

Jaridar ta ce Lucius Iwejuru Ugorji ya roki Muhammadu Buhari ya dage wajen ganin INEC ta sauke nauyinta na shirya zabe na gaskiya da adalci a bana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatarwa Da Yan Nigeria Zai Ai Zabe A Watan Gobe Mai Kamawa

A jawabin da Femi Adesina ya fitar bayan haduwar Buhari da fastocin, an ji shi yana bayanin yadda aka fito da Boko Haram da nufin a wargaza Najeriya.

Zabe na nan a ranar da aka tsaida

Tun bayan lokacin, an ji labari cewa Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed ya karyata batun, ya ce a daina samun wata fargaba.

Haka zalika hukumar zabe watau INEC ta jaddada cewa ba za a fasa yin zabe a watannin Fubrairu da Maris ba, ta ce tuni kayan aiki sun fara isowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng