Tinubu Ya Yi Zama da ‘Yan Kwamitinsa, APC Ta Fara Shiga Kawance da Wasu Jam'iyyu
- Asiwaju Bola Tinubu ya zauna da Gwamnonin Jihohin APC da kwamitin da ke taya shi yakin neman zabe
- A karshe an gyara dabarun da Jam’iyyar APC za tayi amfani da su wajen ganin Bola Tinubu ya yi nasara
- APC ta fara duba yiwuwar hada-kai da wasu ‘yan takara da ‘yan kananan jam’iyyu domin ta kai labari
Abuja - An yi wani zama tsakanin Asiwaju Bola Tinubu, Gwamnonin APC da wasu ‘yan kwamitn yakin neman zabe a kan yadda za a tunkari 2023.
Kamar yadda Vangaurd ta kawo rahoto a ranar Talata, an yi kwana biyu ana zama da ‘dan takaran APC na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Tun ranar Litinin aka soma wannan zama, ba a gama sai safiyar Talata. Sanata Kashim Shettima, Gwamnonin Jihohi da ‘Yan PCC sun samu halarta.
Makasudin zaman shi ne a duba yadda jam’iyyar APC mai mulki za tayi nasara a zabe mai zuwa, an duba tsarin kamfe a jihohi da makamantansu.
PCC ta na dinke baraka a APC
Rahoton ya ce a wannan zama da aka yi, an duba batun yadda wasu daga cikin jagororin jam’iyya suka yi watsi da yakin neman zaben Bola Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A karshen taron, an cin ma matsaya cewa za a hada kai wajen ganin ‘dan takaran ya yi galaba a zaben na Fubrairu, ya gaji kujerar Muhammadu Buhari.
Wata majiya ta ce ‘dan takaran ya yi amfani da wannan dama, ya godewa Gwamnonin APC tare da yin kira a gare su da su mara masa baya sosai.
Gwamnoni akalla 8 sun halarci zaman
A wajen taron akwai Gwamnonin Kebbi, Jigawa, Kaduna, Gombe, Kogi, Zamfara, Ebonyi, Kwara da wasu daga cikin shugabannin kwamitin PCC na APC.
Daga baya rahoton Punch ya nuna kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC yana shirin hada-kai da sauran kananan jam’iyyu domin yin galaba.
Kwamitin PCC yana ganin cewa wannan hadin-kai zai taimakawa takarar Asiwaju Bola Tinubu a kan Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Shrin da aka fito da shi - 'Dan PCC
Sanata Adesoji Akanbi wanda yana cikin ‘yan kwamitin PCC ya shaidawa jaridar su na duba yadda kananan jam’iyyu za su goyi bayan ‘dan takaran na APC.
Sanata Akanbi ya ce su na tattaunawa da jam’iyyun Accord Party, SDP da wasunsu domin su ayyana Tinubu a matsayin wanda magoya bayansu za su zaba.
Amma wasu daga cikin masu neman shugabancin Najeriya irinsu Omoyele Sowore da shugaban APGA sun nuna sam ba za su dunkule da jam’iyyar APC ba.
Tazarcen wasu Gwamnoni a 2023
Kun samu rahoto cewa a irinsu Legas, Borno, Zamfara, Bauchi, Adamawa, Gombe da Oyo, Gwamnoninsu za su gwabza wajen neman kujerar tazarce a bana.
Siyasar Bauchi, 'Yan Bala Must Go, Rikicin Makinde v Atiku, takarar Mace a Adamawa da Jam'iyyar NNPP su na yi wa wasu Gwamnonin barazana.
Asali: Legit.ng