Kotu Ta Kori Sanata Elisha Abbo Daga Neman Takara a Inuwar APC
- Babbar Kotun Yola, Adamawa ta haramtawa Sanata Elisha Abo takarar Sanatan Adamawa ta arewa a zaben Fabrairu
- Mai shari'a Muhammed Danladi yace APC ta kori Sanatan daga inuwarta tun a watan Oktoba, 2022
- Lauyan dake kare wanda ake kara yace zai sanarwa Sanata Abbo hukuncin da Kotu ta yanke kafin su dauki mataki na gaba
Yola, Adamawa - Babbar Kotun Yola karkashin mai shari'a Mohammed Danladi, a ranar Talata ta tsige Sanata Elisha Abbo daga matsayin dan takarar APC a mazabar Adamawa ta arewa a zaben Fabrairu.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bisa hujjar cewa APC a gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Mubi, ta kore shi daga jam'iyar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2022
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mai shari'a Danladi yace har yanzu Sanata Abbo na kan wannan matakin da APC a karamar hukumar Mubi ta dauka a kansa.
Alkalin ya bayyana cewa bisa haka Sanatan bai da hurumin samun wata dama ko alfarma da mambobin jam'iyyar APC ke da ikon samu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta gano cewa a watan Oktoba, shugabannin jam'iyyar suka amince da batun korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na APC ya ba da shawari a rahotonsa.
Abubuwan da Hukuncin Kotu ya kunsa
Bayan haka, Kotun mai zama a Yola ta yanke hana jam'iyyar APC, wacce Sanata Abbo ke neman tazarce a kujerarsa daga daukarsa a matsayin ɗan takararta a zaben 2023.
Haka zalika Hukuncin ya haramta wa Sanatan ya cigaba da bayyana kansa a matsayin dan takarar Sanata a wannan mazaba. Alkali yace masu kara sun gamsar da Kotu da hujjoji.
Yace karar da aka shigar da Sanatan ba harkokin cikin gida na jam'iyar siyasa bane kuma wadan da suka gurfanar da shi suna da hurumin yin hakan saboda su mambobi ne masu rijista.
Shin wanda ake kara ya amince da hukuncin?
Lauyan dake kare Sanatan, E. O. Odo, yace zai sanar da Sanatan hukuncin da Kotu ta yanke idan kuma ya amince zasu wuce zuwa Kotun daukaka kara, kamar yadda Channels ta ruwaito.
A wani labarin kuma An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023
Abdulmumin Jibrin, kakakin kamfen NNPP yace yan arewa kaso 70 zuwa 80 cikin Ɗari sun dawo daga rakiyar jam'iyyar APC.
Tsohon dan majalisar yace Kwankwaso zai kwashe dukka kuri'un arewa ya tsakuro na kudu kuma ya yi nasara a zaben 2023.
Asali: Legit.ng