Dalilin Da Yasa Buhari Zabi Yi Wa Tinubu Kamfe a Jihohi 10 Kacal, Tsohon Sakataren APC
- Babban Jigon APC kuma tsohon Sakataren tsare-tsare ya bayyana dalilin Buhari na yanke zuwa jihohi 10 kamfe
- Farfesa Ussiju Medaner, yace kowa ya san shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tun a baya da kuma masoyan da yake da su
- A cewarsa, yana ganin zai je jihihin ne domin duba muhimman abubuwa da suka shafi talakawa
Tsohon Sakataren tsare-tsare na APC kuma babban Jigo, Farfesa Ussiju Medaner, ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yanke tallata takarar Tinubu a jihohi 10 ne saboda kara karafafa jam'iyya.
Daily Trust ta ce tun da APC ta fara gangamin yakin neman zabe, da yawan 'yan Najeriya sun nuna shakku kan rashin ganin shugaba Buhari a wuraren Ralin.
Sai dai a yanzun kwamitin kamfen dan takarar shugaban kasa na APC ya sanar da cewa Buhari zai halarci tarukan kamfe a jihohi 10 kaɗai.
Da take martani, jam'iyar adawa ta kasa PDP tace matakin shugaban kasa Buhari na zuwa tallata Tinubu a jihohi 10 kacal bai zo mata da mamaki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar babbar jam'iyyar hamayya, hakan ya kara fito da zargin cewa matsa wa shugaban aka yi ya nuna goyon bayan ga tsohon gwamnan Legas.
Meyasa Buhari ya zabi jihohi 10 kadai?
Da yake hira da Arise TV kan cigaban, Farfesa Medaner, yace Buhari ya yanke zuwa jihohi 10 ne kadai saboda ya duba abinda aka yi da kuma abubuwan da ya rage.
A kalamansa, tsohon Sakataren APC ya ce:
"Kun san shugaban kasa ya baiwa mambobin majalisar zartaswa umarni, ina nufin Ministoci, idan kuka duba umarnin ina tunanin wata dabara ce ta tsaftace kamfe. Yanzu kamfe ya kankama kuma bai ragi shugabanci ba."
"Dangane da ɗaga darajar kamfe, ku tuna shugaban kasa a 2003, 2015 da 2019, a zahirin gaskiya yana da daraja kuma yana da masoyan asali a killace, sabida haka zai karfafa abinda dama akwai shi ne kawai."
"Idan muka dauki jihohin da ya zabi zuwa guda 10, kun san siyasarsa, ku duba yawan adadin, ku duba karfinsu sannan kusan inda zaku ta da gardama. Ina tunanin Buhari ya zabi zuwa jihohin ne domn karfafa su."
A rahoton Pulse, Jigon ya kuma bayyana cewa bayan kara masu karfin guiwa Buhari ya zabi su ne domin, "Duba abinda aka yi wa jihohin da kuma duba abinda talakawa ke bukata."
Kwankwaso Ya Dauki Sabbin Alkawurra a Bangaren Ilimi
A wani labarin kuma Kwankwaso ya sha alwashin gina Azuzuwan karatu 500,000 ga yara marasa galihu idan ya ci zabe mai zuwa
Kwankwaso ya yi alkawarin idan aka zabe shi gwamnatinsa zata gina Azuzuwan karatu 500,000 domin yara dake gararamba a Tituna su samu ilimi.
Tsohon gwamnan Kano yace zai inganta jami'o'i da sauran makarantu su yi gogayya a duniya. NNPP ta bude shafin neman tallafin kuɗi na kamfen Kwankwaso.
Asali: Legit.ng