Gwamnati Na Zata Kwashe Yara Marasa Galihu Da Maida Su Makaranta, Kwankwaso
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sha alwashin raba kananan yara miliyan 20m da Titunan Najeriya
- Kwankwaso, mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP, yace da zaran ya ci zabe, gwamnatinsa zata gina dakunan karatu 500,000
- Jam'iyyar NNPP ta kaddamar da shafin taimakon kuɗi da za'a agaza wa kamfen shugaban ƙasa
Abuja - Dan takarar shugaban kasa a inuwar New Nigerian Peoples Party, Rabiu Kwankwaso, yace idan ya ci zabe, gwamnatinsa zata gina Azuzuwan karatu 500,000 ga yara kanana marasa galihu.
Kwankwaso ya dauki wannan alkawarin ne ranar Litinin a wurin kadammar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, (PCC), a birnin tarayya Abuja.
Haka nan Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatinsa zata tabbata manyan makarantun gaba da Sakandire sun kai matakin gogayya a duniya, kamar yadda The Cable ta ruwaito
A kalamansa ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bari na tuna mana cewa a shirye muke mu sauya bangaren ilimi domin mu inganta shi kuma kowa ya samu ikon neman ilimi. Musamman zamu gina Azuzuwa 500,000 a sassan jihohin kasar nan."
"Zamu zuba kananan yara sama da miliyan 20m dake gararamba a sabbin Azuzuwa domin muna da kudirin kawar da su daga yawo a Titunan Najeriya. Zamu maida duk wani Fam na neman gurbi da ɗaukar aiki kyauta."
"Jarabawar gama Sakandire da ta share fagen shiga manyan makarantu kamar WAEC, NECO, NABTEB, NBIAS, JAMB da sauransu zamu maida su kyauta ga 'yan Najeriya."
Da yake tabo Jami'a, kwalejin fasaha da sauran manyan makarantun gaba da sakandire, tsohon gwamnan jihar Kano ya ci gaba da cewa:
"Zamu inganta tare da fadada jami'oi, kwalejojin fasaha, da baki daya kwalejojin mu na ilimi kuma mu daga darajarsu su kai matakin gogayya a duniya.
NNPP ta kaddamar da shafin tallafawa kamfen Kwankwaso
Bayan haka, jam'iyyar NNPP mai kayan daɗi ta kaddamar da bude shafin yanar gizo na hada kuɗi domin taimaka wa yakin neman zaben shugaban kasa.
A wani labarin kuma Kwankwaso ya kaddamar da fara yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar NNPP
Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi kira da daukacin Yan Najeriya su hada hannu da PCC na NNPP domin gina sabuwar Najeriya a watan Mayu mai zuwa.
Dan takarar shugaban kasan ya kuma kara da bayanin jihar da jirgin yakin neman zaben NNPP zai fara sauka da kuma gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta masa.
Asali: Legit.ng