Mahadi Shehu Ya Fede Obasanjo, Ya Tona Boyayyar Hikimar Goyon Bayan Peter Obi

Mahadi Shehu Ya Fede Obasanjo, Ya Tona Boyayyar Hikimar Goyon Bayan Peter Obi

  • Shugaban Dialogue Group ya soki Olusegun Obasanjo saboda yana goyon bayan takarar Peter Obi
  • Mahdi Shehu ya ce tsohon shugaban Najeriya ya dage, yana kokarin tsawaita wa’adinsa a mulki
  • 'Dan kasuwan ya zargi Obasanjo da amfani da salon nan wajen goyon bayan shugabannin baya

Abuja - Mahdi Shehu wanda shi ne shugaban kamfanin Dialogue Group, ya maidawa Olusegun Obasanjo amsa a kan goyon bayansa ga Peter Obi.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin AIT, Alhaji Mahdi Shehu ya fadi abin da yake ganin shi ya sa Olusegun Obasanjo yake tare da Peter Obi.

An jefawa Mahdi Shehu tambaya ko shi ya tsaida ‘dan takara, ganin Obi mai neman zama shugaban kasa a 2023 ya samu mubaya’ar Cif Obasanjo.

‘Dan kasuwan ya ce mubaya’ar Obasanjo ga ‘dan takaran na LP abin dariya ce domin shi kadai ne tsohon shugaban kasar da ke yawan surutu a yau.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon shugaban Najeriya ya tattara dansa sun fece Turai saboda gudun rikicin zabe

Allurar sojar Obasanjo ta tashi

A cewar Mahdi, ya gano abin da ya sa dattijon ya cika ko ina da surutu, dalili kuwa shi ne horaswar da ya samu daga gidan soja a shekarun baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attajirin ya ce har yanzu allurar gidan sojan ba ta saki tsohon shugaban Najeriyan ba, yana jin har gobe zai iya bada umarnin abin da ya kamata ayi.

Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo a Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A bidiyon hirar, an ji Mahdi Shehu yana cewa an san soja ne da yin kwantar bauna, mamaya da fadan sunkuru, ba su fito bara-baro domin a gwabza ba.

Haka zalika siyasa tamkar yaki ne ba tare da amfani da makami ba, a ra’ayin Shehu.

Obasanjo bai hakura da tazarce ba

"Kuma ina tunanin yana kokarin ganin ya samu wa’adinsa na uku ne ta hanyar goyon bayan Peter Obi, kuma bai koyi darasi ba.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

A salon da ya kawo Shugaba ‘Yar’adua, ya dauka zai juya shi, amma ‘Yar’adua ya yi masa taurin-kai, haka ya kawo Jonathan.
Shi ma Shugaba Jonathan ya kauce ya kyale shi, a irin haka ne ya goyi bayan Muhammadu Buhari, a yanzu yana fada da shi.

- Mahadi Shehu

Tsohon malamin asibitin yana ganin Obasanjo ya rasa kimarsa a dalilin nuna ra’ayinsa a fili, ya ce a matsayinsa na jagora, yin hakan bai dace ba.

Obasanjo ya bi LP - Mahadi

Idan ku na biye da mu, tun a tsakiyar shekarar 2022 aka ji Mahadi Shehu ya ce Olusegun Obasanjo yana cikin masu mara baya ga takarar Peter Obi.

A wata hira da aka yi da shi, Mahadi Shehu ya ce makasudin zuwan Olusegun Obasanjo Arewa a Yulin 2022 shi ne tallata Obi ga dattawan yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng