Allah Ne Kadai Zai Iya Dakatar da Tinubu a Burinsa Na Zama Shugaban Kasa, Sule

Allah Ne Kadai Zai Iya Dakatar da Tinubu a Burinsa Na Zama Shugaban Kasa, Sule

  • Gwamna Abdullahi Sule yace ba wanda zai iya hana Tinubu zama shugaban kasa a zaben 2023 sai Allah madaukakin sarki
  • Gwamnan na jihar Nasarawa kuma mamban APC ya karyata jita-jitar wasu gwamnoni na tattauna wa da Atiku Abubakar
  • A cewarsa, gwamnonin arewa na APC ne suka tsaya kai da fata aka tsaida Tinubu, zasu yi duk me yuwuwa ya samu nasara

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Allah ne kadai zai iya dakatar da Bola Ahmed Tinubu daga zama magajin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Sule ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin kaddamar da kamfen dan takarar Sanatan Nasarawa ta yamma a inuwar APC, Shehu Tukur, wanda ya gudana a karamar hukumar Kokona.

Gwamna Abdullahi sule.
Allah Ne Kadai Zai Iya Dakatar da Tinubu a Burinsa Na Zama Shugaban Kasa, Sule Hoto: Abdullahi Sule/facebook
Asali: Facebook

Gwamna Sule ya ce takwarorinsa gwamnonin arewa na APC zasu yi amfani da dukiyarsu wurin tabbatar da Bola Tinubu ya lashe babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Ministan Buhari Ya Tona Asirin Wasu Shugabannin APC Dake Yi Wa Atiku Aiki

Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamnan na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnonin APC na arewa zasu zuba dukiyarsu domin tabbatar da Tinubu ya zama shugaban kasa, idan akwai masu kaunar Tinubu ya zama magajin Buhari a sahun farko to gwamnonin arewa ne."
"Allah ne kadai zai iya hana Tinubu da Abdullahi Sule zama shugaban kasa da gwamna. Mun shirya zuba dukiyarmu da karfinmu damin mu binne duk wani hankoron yan adawa."
"Burinmu mu ga Tinubu, Sanatoci uku, mambobin majalisar wakilan tarayya biyar da mambobin majalisar dokokin jiha 24 sun zama zababbu a wata mai zuwa."

Shin da gaske ne gwamnonin APC 11 na tare da Atiku?

Bugu da kari, Sule ya musanta rahoton da ke cewa gwamnonin APC 11 na tattauna wa a boye da dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar.

"Wannan karya ce tsagwaronta, gwamnonin arewa a APC ne suka matsa har Tinubu ya zama dan takara, zasu yi duk me yuwuwa su tabbatar ya zama shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo da Atiku Ya Tono Zunubinsu Na Baya

"Ku yu watsi da irin wadan nan karerayin dake fitowa daga bakunan masu neman alfarmar Tinubu."

A wani labarin kuma Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi Ya Gaji Buhari a 2023

Peter Obi ya yi alkawarin cewa idan har yan Najeriya suka ba shi amana a 2023, to zai ji tsoron Allah a gwamnatinsa.

Dan takarar na LP yace PDP da APC da suka mulki kasa sun lalata komai, matasa ba aiki, hanyoyin ba tsaro, ga tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel