'Yan Adamawa Sun Cika da Farin Ciki, Sun Taru Don Tarbar Buhari Yayin Ziyarar Kamfen
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Yola, babban birnin jihar Adamawa don kaddamar da yakin neman zabe a jihar
- Ziyarar da Shugaban kasar ya sa cikin yan PDP ya duri ruwa kasancewar jihar ita ce mahaifar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar
- Aishatu Binani, yar takarar gwamnan APC a jihar ita kadai ce mace da ke neman tseren kujerar a zaben 2023
Adamawa- Babban birnin Yola da ke jihar Adamawa ta cika da harkoki yayin da ake jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari don gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A bisa ga wani bidiyo da Bashir Ahmed ya wallafa, Buhari ya isa filin jirgin sama na Yola da misalin karfe 10:30 don halartan taron wanda za a yi a yau Litinin, 9 ga watan Janairu.
Jaridar PM News ta rahoto cewa an tsaurara matakan tsaro yayin da aka zuba Jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a ciki da wajen filin wasa na Mahmud Ribadu Square wanda a nan za a yi taron.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana sa ran Buhari zai kai ziyarar bangirma ga sarkin jihar kuma Lamidon Adamawa, Alhaji Barkindo Aliyu Mustapha, inda daga nan zai tafi wajen taron.
Yan siyasa da masu fatan alkhairi, musamman masu biyayya ya APC sun taru don tarban babban bakon.
Zuwan Buhari zai kara daukaka darajan yan takarar APC, Tadawus
Mista Samaila Tadawus, shugaban APC a jihar, ya nuna yakinin cewa zuwan shugaban kasar jihar zai kara karfafa damar da jam’iyyar ke da shi a zabe.
Ya ce kasancewar Buhari a wajen zai kara daraja ga yan takarar jam’iyyar mai mulki.
Tadawus ya ce jam’iyyar ta dauki hanyar yin nasara a dukkanin zabukan, musamman a zaben gwamnan jihar inda yar takara mace, Sanata Aishatu Binani ke neman shugabanci.
Wannan shine karo na farko da Buhari zai bayyana a wajen kamfen kuma a jihar Adamawa wacce take mahaifar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Kalli bidiyon isowarsa a kasa:
A wani labari a daban, an bukaci ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da ya baiwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu hakuri don samun maslaha a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng