Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

  • Sanata Yaroe Binos ya shaida cewa sai da aka bijiro da maganar tunbuke shugaban kasa a majalisa
  • ‘Dan majalisar dattawan ya ce sun koka a kan yadda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke lafto bashi
  • Duk abin da zai faru, Binos ya sha alwashin ba za su bada dama bashin da ake bin kasar ya kai N70tr ba

Abuja - Sanata Yaroe Binos mai wakiltar mazabar Kudancin jihar Adamawa a majalisar dattawa, ya bada labarin yunkurin da aka yi na tsige shugaban kasa.

Punch ta rahoto Sanata Yaroe Binos ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya sun nemi su tunbuke Muhammadu Buhari saboda yawan karbo bashinsa.

Sanatan yake cewa an bijiro da wannan magana a ranar da aka amince da kasafin kudin 2023.

A zantawar da ya yi da kungiyar ‘yan jarida na Adamawa, Binos bai kama sunan ‘yan majalisar kasar da suka kawo maganar tsige Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

An Fadi Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan da Zai Iya Biyan Bashin Da Ake Bin Najeriya Idan Ya Ci Zaben 2023

APC za ta bar tulin bashi

‘Dan majalisar ya yi hira da wakilan NUJ a karshen makon nan, inda aka ji ya koka a kan bashin da Mai girma Muhammadu Buhari zai bari a Mayun 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ake tattaunawa a kan kasafin kudin N21.82tr na sabuwar shekarar nan, wasu ‘yan majalisa sun nuna bashin N22tr da CBN yake bin gwamnati ya saba doka.

Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan Hoto: @NgrSenate
Asali: Twitter

A majalisa, akwai masu ra’ayin aron kudin da gwamnatin Buhari tayi daga 2015 zuwa yanzu ya wuce gona da iri, ya kamata a sauke shi daga kan mulki.

Jaridar ta ce Sanatan Kudancin Adamawan ya ce kudin da ake bin Najeriya bashi ya kai N47tr, adadin zai iya haura N70tr idan suka amince da wasu karin.

Ana asarar bashin da aka karba

‘Dan siyasar ya soki yadda gwamnatin tarayya ta ke amfani da kudin da ta aro, ya ce ba a batar da duka abin da aka ci bashin wajen ayyukan more rayuwa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Kotu ta yanke hukunci kan bukatar a tsige shugaban INEC, a bincike dukiyarsa

Zargin da Binos yake yi shi ne wani kaso na bashin da aka karbo yana tafiya ne wajen hidindimun yau da kullum, a karshe sai a bar ‘yan baya da bashin.

‘Dan majalisar ya ce abokan aikinsa da suka gaji da zargin da ake yi masu na zama ‘yan amshin shata, sun sha alwashi ba za a biyawa shugaban kasa bukata ba.

Ba tare da la’akari da jam’iyya ba, Sanatan ya ce sun hadu a kan rashin amincewa da canza tsarin bashin CBN wanda zai sa kudin da ake bin Najeriya ya kai N70tr.

Rikicin PDP a Ribas

An ji labari cewa, jam’iyyar PDP ta biya makudan miliyoyi ga Gwamnatin jihar Ribas domin a mallaki izini na wuraren yin yawon kamfe na zabe mai zuwa.

Amma da alama duk da kudin da aka karba, ‘dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar bai da damar da aka ba sauran masu neman takara na kamfe.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami’an DSS Sun Kama Kwamandan ISWAP da ya Dasa Bama Ranar da Buhari zai Sauka Kogi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng