Wasu Shugabannin APC Na Yi Wa Atiku Aiki a Akwa Ibom, Sanata Akpabio
- Tsohon ministan Buhari, Sanata Godswil Akpabio, ya zargi wasu shugabannin APC da cin amana a boye
- Akpabio, mataimakin shugaban kwamitin kamfen APC na kasa, ya karbi wasu kungiyoyi 250 da suka shirya marawa Tinubu baya
- Yace a shirye yake ya tallafi duk wadan da zasu ce sai Tinubu, amma ba masu kiran Asiwaju da rana su koma Atiku da daddare ba
Akwa Ibom - Mataimakin shugaban kwamitin kamfen APC na kasa, Sanata Godswill Akpabio, ya fallasa cewa wasu daga cikin shugabanni jam'iyya na yi wa Atiku Abubakar aiki a boye.
Akpabio yace shugabannin APC a jihar Akwa Ibom na babatun, "Sai Asiwaju da rana yayin da daddare kuma su koma sai Atiku." kamar yadda Punch ta ruwaito.
Tsohon ministan Neja Delta, wanda ya yi murabus domin neman takara, ya fadi haka ne a karamar hukumar Ikot Ekpene yayin da ya karbi bakuncin kungiyoyi 250 dake goyon bayan Bola Tinbu.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Jackson Udom, ya fitar ranar Asabar, ya zargi jagororin APC reshen Akwa Ibom da rashin ɗa'a da kokarin ruguza jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan ta hakaito Akpabio na cewa:
"Na yi farin ciki da zuwan wadan nan kungiyoyi kuma na yi murna mara misaltuwa da suka yanke ba da gudummuwa don ganin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa da sauran yan takarar APC sun kai ga nasara."
"A wuri na wadan nan kungiyoyin sune tushen manufar da muka sa a gaba, ina kallonku a matsayin mutane na gaske da suka shirya sadaukarwa, dama na zo ne idona ya gane mun kuma na gani na gamsu."
"Na ji labarin wasu shugabanni sun kafa kungiyoyi a cikin APC duk don marawa dan takararmu baya, bana adawa da su, matukar dan jam'iyya aka kafa su zan halarci taronsu idan ina gari."
Wasu a fatar baki kawai suke tare da Tinubu - Akpabio
Amma a cewar Sanatan ba zai goyi bayan wurin da ya san ana cin amanar jam'iyyarsa ta APC ba, inda ya kara da cewa:
"Wurin da ba za'a ga kafa ta ba shi ne yanayin yadda wasu shugabannin APC a jiha ke tare da Asiwaju da rana amma da zaran dare ya yi sai su koma PDP."
"Akwai wanda na sani ya ayyana goyon baya ga dan takarar gwamna da Sanata na PDP, amma ya ruga Uyo yana cewa shi ne shugaban Ralin Tinubu, wane Tinubu yake nufi?"
A wani labarin kuma Gwamnan Filato Ya Bayyana dalilan da zasu ja ra'ayin mutame su sake amincewa da APC a 2023
Gwamnan Filato yace mulkin APC ya samar da zaman lafiya, ci gaba da kwatanta adalci don haka mutane ba zasu juya mata baya ba a zabe.
Simon Lalong yace wadan nan abubuwa zasu ja hankalin mazauna Filato, da sauran jihohin Najeriya su zabi APC sak a zabe na gaba.
Asali: Legit.ng