Zaben 2023: Labour Party Ta Bayyana Dabarar Da Obi Zai Yi Amfani Da Ita Don Samun Nasarar Zama Shugaban Kasa

Zaben 2023: Labour Party Ta Bayyana Dabarar Da Obi Zai Yi Amfani Da Ita Don Samun Nasarar Zama Shugaban Kasa

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, yana dogara ne ga talakawan Najeriya don nasara a zabe
  • Yinusa Tanko, mai magana da yawun kungiyar kamfen din Obi-Datti ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a 6 ga watan Janairu
  • Tanko ya ce Obi shine dan takarar mafi cancanta cikin wadanda suka fito neman shugaban kasa shi yasa yan Najeriya ke daukan nauyin kamfen dinsa

Mai magana da yawun kungiyar kamfen din jam'iyyar Labour ya yi magana kan dabarar da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ya dogara da ita don nasara a zaben da ke tafe.

Yinusa Tanko, kakakin kungiyar kamfen din Obi-Datti, a ranar Juma'a 6 ga watan Janairu ya bayyana cewa Obi ya dogara ne da talakawan Najeriya don cin zabe, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce Ba Za a Gani a Kasa Ba, Tinubu Kan Alkawaran Zaben da Atiku da PDP Suka Daukarwa Yan Najeriya

Peter Obi
Zaben 2023: Labour Party Ta Bayyana Dabarar Da Obi Zai Yi Amfani Da Ita Ya Ci Zabe. Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Tanko ya ce 'structure' da jam'iyyar da dan takarar shugaban kasarta ke magana a kai shine matasa, masu sana'o'in hannu, kungiyar kwadago, NLC, kungiyar TUC, da talakawan Najeriya da ke fatan ganin mulki na gari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa jam'iyyar ta tattara kan wadannan bangarorin gabanin zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Hakazalika, Tanko ya bigi kirji yana mai cikin dukkan manyan yan takarar, Obi shine mafi cancanta shi yasa ba ya kokarin siyan kuri'un talakawa.

Kalamansa:

"Cikin dukkan yan takarar, Obi kadai yan Najeriya suka yarda da shi, shine kadai dan takarar da baya siyan kuri'u, za ka ga irin kauna da matasa da yan Najeriya ke nuna masa suna kashe kudinsu don kamfen dinsa.
"Obi yana da kwarewa da hali mai kyau da tausayi da jajircewa don gina kasa. Ya ce zai sauya kasar daga cima zaune zuwa mai kirkirar abubuwa. Shine kadai gwamnan da ya bar naira biliyan 75 a baitil malin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Hantar Tinubu, Atiku Da Obi Na Kaɗawa Yayin Da G5 Suka Dira Ibadan Don Sanar Da Wanda Za Su Marawa Baya

"Za mu mamaye Freedom Park da ke tsakiyar garin Osogbo don kamfen din Obi. Akwai kungiyoyin goyon bayan Peter Obi masu yawa a jihar Osun kuma fiye da kashi 71 cikin dari na matasan Najeriya na tare da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel