Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban YPP Na Gunduma a Jihar Imo

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban YPP Na Gunduma a Jihar Imo

  • Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton Yan Banga ne sun harbe shugaban YPP na gundumar Ibeme a jihar Imo
  • Wani ganau ya bayyana cewa maharan sun yi ajalin dan siyasan ne a kofar gidan iyalansa ranar Laraba da ta gabata
  • Shugaban YPP na jihar Imo, Victor Diala, ya tabbatar da faruwar lamarin amma har yanzun 'yan sanda ba su ce komai ba

Imo - Wasu miyagun 'yan bindiga da ba'a san manufarsu ba sun yi ajalin shugaban Young Progressives Party (YPP) na gundumar Ibeme da ke karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo, David Uche.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa 'yan ta'addan sun bindige jigon siyasar har lahira a gaban gidan iyalansa da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Laraba da ta gabata.

Shugaban YPP.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban YPP Na Gunduma a Jihar Imo Hoto: thenationonline
Asali: UGC

A cewar wani da lamarin ya faru a kan idonsa, yan bindigan, wadan da ake zaton 'yan banga ne sun farmake sa ne a cikin motoci biyu, motar Sienna da kuma Lexus 300.

Kara karanta wannan

Ba Don Shugaba Buhari Ba, Da Tuni Jihata Ta Tarwatse, Gwamna Ya Fayyace Gaskiya

Bayanai sun nuna cewa ana zargin wani mutumi wanda ya zo bin ba'asin bashi na N100,000 ne ya dauki hayar 'yan bangan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban jam'iyyar YPP na jihar Imo, daya daga cikim jihohin kudu maso gabashin Najeriya, Mista Victor Diala, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Mista Diala ya yi bayanin cewa:

"Eh tabbas lamarin ya auku, an harbe matashin dan siyasan a gaban gidan iyalansa."
"Abun dariya da ban mamakin shi ne makasan ne suka dauki gawarsa zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Owerri (babban birnin Imo), inda suka shafa masa kashin cewa d'an bindiga ne da ba'a sani ba."

Yayin da aka tuntubi Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Imo, Michael Abattam, ba'a same shi ba domin jin ta bakinsa game da lamarin.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

An Kashe Shugaban PDP da Yayansa a Sakkwato

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Sakkwato

Miyagun yan bindiga da ba'a san su ba sun yi wa shugaban PDP na gundumar Asare jihar Sakkwato yankan rago bayan dawowa daga Kamfe.

Rahotanni sun bayyana maharan sun hada da yayan jirgon siyasan yayin da ya yi yunkurin kaiwa dan uwansa dauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel