2023: A Karshe, Atiku, PDP Sun Samu Sako Mai Karfafa Zuciya Daga Gwamnonin G5
- Gwamnonin Peoples Democratic Party, PDP na G5 sun jadada matsayinsu kan jam'iyyar da za su mara wa baya a babban zaben da ke tafe
- A cewar gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, kungiyar tasu za ta tabbatar sun samu nasara a jihohinsu yayin zaben
- Ortom wanda ya bayyana hakan bayan kamfen din tazarcen Seyi Makinde a Oyo a ranar Alhamis, ranar 6 ga watan Janairu, ya ce gwamnonin na G5 mutanen kirki ne
Gwamna Samuel Ortom na jihar Ortom ya yi magana da zai iya bawa Atiku Abubakar kwarin gwiwa da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Ortom, a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, ya ce shi da takwarorinsa a PDP na G5 ba za su yi watsi da jam'iyyarsu ba, New Telegraph ta rahoto.
2023: Magana Ta Kare, Wike da Ortom Sun Hada Baki, Sun Yi Magana Kan Dan Takarar da G5 Zata Marawa Baya
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP aka zabi gwamnonin na G5 kuma har yanzu su yan jam'iyya na masu kishinta.
Gwamnan na Benue ya yi wannan jawabin ne bayan kaddamar da yakin zaben tazarcen Gwamna Seyi Makinde a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Daily Post ta rahoto.
A wani sanarwar da babban sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar, Ortom ya ce gwamnonin na G5 za su yi aiki tukuru don ganin PDP ta yi nasara a jihohinsu a babban zaben da ke tafe.
A cewarsa:
"Shi da sauran mambobin na PDP a jihohinsu za su yi aiki don tabbatar da cewa jam'iyyar ta yi nasara."
Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Gwamnonin G5 Ba Za Su Fita Daga Jam'iyyar PDP Ba, In ji Jibrin
A wani rahoton, Sanata Walid Jibrin, tsohon shugaban kwamitin amintattu ,BoT, na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa ya ce gwamnonin G5 ba za su fice daga jam'iyyar PDP ba.
Gwamnonin na G5 sun samu matsala da uwar jam'iyyar ne tun bayan da Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa kuma suka bukaci Iyorchia Ayu, ciyaman din jam'iyya ya sauka.
Gwamnonin da suka hada da Nyesom Wike na Rivers, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi na Enugu sun dage dole shugabancin jam'iyyar ya koma kudu.
Asali: Legit.ng