Taron Kano Ya Tabbatar da Cewa Tinubu Ba Shi da Wani Abin da Zai Tsinanawa ’Yan Najeriya, Cewar Atiku
- Jam’iyyar PDP mai adawa har yanzu bata gama caccakar gwamnatin APC ta su Buhari mai mulki ba
- Wannan kuwa ya faru ne a lokacin da Bola Tinubu ya kai ziyarar kamfen a jihar Kano, Atiku yace Tinubu ya ba zai tsinana komai ba
- A bangare guda, Tinubu ya yiwa ‘yan Najeriya alkawura masu yawa yayin da ya tara dandazon jama’ar da suka yi maraba dashi a jihar
A cewar Atiku, ganin yadda Tinubu ya gaza yin wata magana mai daukar hankali a gaban jama’a a jihar Kano, hakan ya nuna ba zai yiwa ‘yan Najeriya abin kirki ba idan ya gaji Buhari.
Ya bayyana hakan ne bayan da Tinubu ya tara jama’aa Kano a ranar Laraba 4 ga watan Janairu a wani babban taron kamfen da aka yi.
Atiku ya caccaki Tinubun ne a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa Phrank Shaibu.
Atiku ya yi kaca-kaca da Tinubu bayan kamfen Kani
Nigerian Tribune reported that it said after spending so much money to organise a rally in Kano State, Tinubu could not even manage to say anything meaningful.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an ce bayan kashe manyan kudade wajen shirya taron kamfen na Kano, Tinubu ya gaza fadin wata magana mai ma’ana a wurin taron.
Tsagin Atiku ya kuma bayyana cewa, a madadin ya yi magana mai ma’ana, Tinubu ya dage sai tikar rawa kawai a filin taron, rahoron Daily Sun.
Abin takaici Tinubu na tika rawa, inji PDP
Sanarwar ta ce:
“Abin takaici, Tinubu tika rawar Tinubu ya nuna rashin kamun kai da kuma maganarsa marar ma’ana, Mutane da iyayen giji ma sun yi nesa dashi.”
Haka nan, sanarwar ta kuma yi tsokaci ga halin lafiyar Tinubu, inda tace kamata ya yi ace yanzu kam yana can yana kula da lafiyarsa.
An karya Tinubu, jiga-jigan APC sun koma PDP
A wani labarin, wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun bayyana ficewa tare da komawa jam'iyyar PDP ta dawa.
Akalla mutum 3000 ne suka bayyana sauya sheka a jihar Kogi, inda suka bi sahun tsohon kakakin majalisar dokokin jihar.
Ana ci gaba da fuskantar sauya sheka a Najeriya tun bayan da aka fara gangamin kamfen zaben 2023 da ke tafe.
Asali: Legit.ng