Jigon PDP Ya Bada 'Hujjar' Cewa Gwamnonin Arewa Na APC 11, Da Sanatoci Fiye Da 30 Suna Wa Atiku Aiki

Jigon PDP Ya Bada 'Hujjar' Cewa Gwamnonin Arewa Na APC 11, Da Sanatoci Fiye Da 30 Suna Wa Atiku Aiki

  • Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa, Daniel Bwala ya dage, ya ce wasu gwamnoni da sanatocin APC suna yi wa Atiku aiki
  • Bwala ya ce dalilin shine yadda mutane ke cigaba da amsawa da 'Atiku' duk lokacin da aka yi ihun 'Najeriya' a kamfen din shugaban kasa na APC
  • Kakakin na kamfen din Atiku-Okowa wanda ya yi magana da Arise TV a ranar Alhamis, ranar 5 ga watan Janairu, ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa Atiku ne zai ci zaben shugaban kasa na 2023

Daniel Bwala, kakakin kamfen din shugaban kasa na Atiku-Okowa ya jadada cewa wasu gwamnonin arewa da sanatoci yan jam'iyyar APC suna yi wa Atiku Abubakar, dan takarar PDP aiki a boye.

Bwala ya kuma bayyana kwarin gwiwa cewa bisa dukkan alamu Atiku ne zai lashe zaben shugaban kasan da ke tafe.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe, Atiku, PDP Sun Samu Sako Mai Karfafa Zuciya Daga Gwamnonin G5

Atiku da Tinunu
Jigon PDP Ya Bada 'Hujjar' Cewa Gwamnonin Arewa Na APC 11, Da Sanatoci Fiye Da 30 Suna Wa Atiku Aiki. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya yi watsi da zargin cewa wasu gwamnonin APC na yi wa Atiku aiki, Bwala, a ranar Alhamis, a watan Janairu ya ce yana kan bakansa.

Da ya ke magana a hirar da aka yi da shi a Arise Television, Bwala ya ce:

"Gwamonin jam'iyyar APC guda 11 da sanatoci 35 zuwa 37 suna yi wa Atiku aiki a boye."

Kakakin na PDP ya ce dalilinsa shine yadda mutane suke bada amsa da "Atiku" duk lokacin da aka ce "Najeriya" a wurin kamfen din APC.

Bwala ya ce:

"Idan ka lura a baya-bayan nan, a kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, idan sun ce Najeriya, mutane sai su amsa da cewa Atiku. Shi yasa a kamfen dinsu na karshe a Kano a ranar Laraba, sun dena cewa Najeriya domin tabbas mutane za su amsa da Atiku."

Kara karanta wannan

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

Da aka matsa masa ya ambaci suna wasu cikin wadanda ke yi wa Atikun aiki, ya ki, yana mai cewa:

"Ko yaro na dan shekara hudu ya san ba a fadan irin wannan abin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel