2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, tana cike da kwarin gwiwa kan cewa ita za ta lashe zaben shugaban kasa na 2023
  • Dr Daniel Bwala, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya ce babu yadda za a yi APC ta ci zaben 2023
  • Ya bayyana cewa yan Najeriya sun dawo rakiyar APC kuma babu yadda za a yi su sake danka mata amana bayan gazawa na shekara bakwai a gwamnati

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku/Okowa, Dr Daniel Bwala ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ba zai iya cin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu ba.

Bwala ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da cewa yayin da ya ke kwatanta yiwuwar samun nasara tsakanin Tinubu da mai gidansa a zaben na Fabrairu.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Ya Bada 'Hujjar' Cewa Gwamnonin Arewa Na APC 11, Da Sanatoci Fiye Da 30 Suna Wa Atiku Aiki

Asiwaju
2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa babban dalilin da zai kayar da APC a zaben shugaban kasar shine yan Najeriya ba za su sake yarda da su ba bayan gazawa na wa'adi biyu.

Kwararren a bangaren shari'a ya ce rashin yarda daga yan Najeriya shine abin da APC ke fuskanta.

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, an ambato Bwala na cewa:

"Rashin yarda daga yan Najeriya shine abin da ke adabar APC. Shi yasa suka dauki lokaci mai tsawo kafin fara kamfen. Akwai rashin yarda da hadin kai tsakanin kamfen din Asiwaju (Tinubu), jam'iyyar da gwamnoni kuma mutanen kasa sun sani. Ko bayan fara kamfen, babu yarda tsakaninsu.
"Wannan shine dalilin da yasa Asiwaju ya ki sakin kudaden kamfen da direktoci suka bukata.
"Ko lokacin da suka kira gwamnonin G-5 na PDP taronsu a Landan, ba su cimma matsaya ba saboda rashin yarda da juna tsakaninsu. Babu yadda za a yi APC ta sayar da kanta a wurin yan Najeriya, a dai yanzu da wani lokaci nan gaba."

Kara karanta wannan

"Gwamnoni 11 da Sanatocin Jam’iyyar APC 35 Suna Yi wa Atiku Aiki a Boye a Arewa"

Bwala ya bayyana shekaru bakwai da suka gabata a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya, yana mai cewa an fi samun yawan mace-mace.

Ya kuma kara da cewa kasar ta samu mummunan matsalar tattalin arziki tun farkon gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164