Kotu ta Dawo da Lawal-Dare Matsayin Halastaccen ‘Dan Takarar Gwamnan Zamfara a PDP

Kotu ta Dawo da Lawal-Dare Matsayin Halastaccen ‘Dan Takarar Gwamnan Zamfara a PDP

  • Wata kotun daukaka kara dake zama a yankin Sokoto, ta tabbatar da Daura Lawal-Dare matsayin halastaccen ‘Dan takarar gwamnan Zamfara a PDP
  • A watan Nuwamban da ya gabata ne wata kotun tarayya da ke zama a Gusau ta kwace takararsa tare da ayyana cewa PDP bata da ‘dan takarar Gwamna a Zamfara a 2023
  • Duk da tun farko Ibrahim Shehu da was mutum biyu sun tunkari kotu inda aka umarci canza zaben fidda gwani kuma dare yayi nasara, kotu ta dake kwace kujerar takarar daga wurinsa

Zamfara - Kotun daukaka kara ta shiyyar Sokoto ta tabbatar da Daura Lawal Dare matsayin ‘dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar Zamfara a zaben 2023, Channels TV ta rahoto.

Lawal-Dare
Kotu ta Dawo da Lawal-Dare Matsayin Halastaccen ‘Dan Takarar Gwamnan Zamfara a PDP. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Hakan na nuna ta soke hukuncin kotun tarayya da ke zama a Gusau wacce da farko ta fatattaki Lawal Dare.

Kara karanta wannan

An ramawa Atiku: Gwamna mai ci da 'yan takarar gwamna 2 sun ki halartar kamfen PDP

A watan Nuwamba, kotun ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP na ‘yan takarar gwamna wanda ya samar da wanda ake kara matsayin ‘dan takara, wanda shi ne karo na biyu da kotun ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar a jihar.

A hukuncin babbar kotun tarayya, tace jam’iyyar PDP bata da ‘dan takarar gwamna a jihar a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A watan Satumba, kotun ta soke zaben fidda gwani na baya da aka zabi Lawal Dare wanda Ibrahim Shehu da wasu ‘yan takara biyu suka kai kara don kalubalantar ingancin zaben fidda gwanin.

Kotun ta bukaci a sake zaben fidda gwani amma Lawal Dare ya sake samun nasara a watan Satumban.

Daily Trust ta rahoto cewa, Dare ya samu kuri'u 431 inda yayi caraf da tikitin takarar gwamnan jihar Zamfara na jam'iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi na ranar 25 ga watan Mayun 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami’an DSS Sun Kama Kwamandan ISWAP da ya Dasa Bama Ranar da Buhari zai Sauka Kogi

Sauran 'yan takarkarin sun hada da Abubakar Nakwada, Wadatu Madawaki da Ibrahin Shehu Gusau wadanda da farko suka janye daga takarar saboda magudi.

Sai dai Adamu Maina, wanda shi ne baturen zaben, yace ba a mince da janyewarsu ba tunda babu takardar da suka bayar matsayin sanarwa.

Uba Sani ya tabbata 'dan takarar gwamnan Kaduna

A wani labari na daban, wata kotun tarayya ta jadda Sanata Uba Sani matsayin halastaccen 'dan takarar gwamnan jihar Kaduna.

Kamar yadda aka gano, Honarabul Sani Sha'aban ne yayi kara kan zaben fidda gwanin da ya samar da Uba Sani matsayin 'dan takaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng