Mubaya’ar da Obasanjo Ya yi wa Peter Obi Ta Jawo Bola Tinubu ya Tona Masa Asiri
- Asiwaju Bola Tinubu ya samu lokaci ya yi raddi a kan mubaya’ar da Olusegun Obasanjo ya yi wa Peter Obi
- ‘Dan takaran shugaban kasan ya ce Obasanjo bai da hurumin da zai fadawa mutane wanda za su zaba a 2023
- Tinubu ya jero yadda Gwamnatin Obasanjo ta kawo masa cikas da yake Gwamnan Legas a 1999 zuwa 2003
Edo - ‘Dan takaran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya maida martani da kansa ga Olusegun Obasanjo a kan tsaida Peter Obi a zaben bana.
The Guardian ta rahoto ‘dan takaran yana cewa Cif Olusegun Obasanjo bai da hurumin da zai fadawa ‘yan Najeriya wanda ya kamata su ba kuri’a.
Bola Tinubu ya yi wannan jawabi yayin da ya je yawon neman shugaban kasa a Benin, jihar Edo.
‘Dan takaran ya bada labarin irin yadda Gwamnatin Olusegun Obasanjo ta kawo masa cikas iri-iri a lokacin da yake rike da kujerar Gwamnan jihar Legas.
Kirkirar kananan hukumomi a Legas
Tinubu yake cewa a lokacin da ya kirkiri sababbin kananan hukumomi domin kawowa Legas cigaba, Obasanjo a sa’ilin yana shugaban kasa, ya taka shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Tinubu, Obasanjo ya karbe masu albashi, ya rike kudin kananan hukumominsu, ya tambaya shin za a kira shi mutumin kirki ne ko mugu.
“Na kawo Enron su magance matsalar wutar lantarki kuma a bunkasa tattalin arzikin Legas amma Obasanjo da PDP suka hana ruwa gudu.
Sai suka azabtar da ni da mutanen Legas, kuma su ka fara zare mana kudinmu.”
- Bola Tinubu
Punch ta rahoto ‘dan takaran na APC yana cewa idan har tsohon shugaban kasar na Najeriya ya fito da ‘dan takararsa, to guba yake kokarin ba al’umma.
Makaho ya zama 'dan jagora
Mubaya’ar da Obasanjo ya yi wa tsohon Gwamnan Anambra watau Peter Obi, tamkar wanda bai san hanya ba ne yake yi wa makahon mutumi ‘dan jagora.
Bola Tinubu bai bar garin Benin ba sai da ya soki babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Obasanjo na PDP.
The Guardian ta ce ‘dan takaran ya ce Atiku ya kama kan shi da ya yi bayanin yadda ya sabawa dokar aikin gwamnati, ya yi kudi da haram a gidan kwatsam.
Neman takara ta jawo alakar Waziri da Gwamna tayi tsami
Ku na da labari Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya rasa sarautar Wazirin Bauchi da matsayin ‘Dan majalisa a fadar Sarki saboda sabaninsa da Gwamna.
Masarautar Bauchi karkashin jagorancin Sarki Rilwanu Suleiman Adamu, ta nada Muhammad Uba Kari a matsayin sabon Waziri bayan abin da ya faru.
Asali: Legit.ng