2023: Ku Janye Ku Barwa Makinde, Gwamna Wike Ya Aike da Sako Dan Takarar APC
- Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya sake aike wa da sako ga jam'iyyar APC da sauran jam'iyyun adawa a jihar Oyo
- Wike, jagoran gwamnonin G5 da suka ja daga a PDP, ya roki duk mai hangen kujerar gwamnan Oyo ya janye kafin zabe
- A cewarsa, gwamna Seyi Makinde, dan takarar PDP ya yi abun a zo a gani a zangon munlkinsa na farko, ya dace a ba shi dama ya dora
Oyo - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya roki baki daya masu neman gwamnan jihar Oyo na jam'iyyun adawa su janye daga takara a zaben 2023.
Jaridar Tribune ta ce Wike ya roki yan takarar ciki har da Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamnan Oyo a inuwar APC su janye wa gwamna Makinde na PDP gabanin zuwan zaben 2023.
Wike ya yi wannan roko ne ranar Alhamis 5 ga watan Janairu, 2023 a wurin gangamin kamfen neman tazarcen Makinde wamda ya gudana a Ibadan, babban birnin Oyo.
A cewar Wike, shugaban tawagar gwamnonin G5 da suka ware kansu a PDP, Makinde ne kadai dan takarar fita kunya, inda ya roki masu katin zabe su jefa wa gwamnan kuri'unsu a zabe mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wike ya ci gaba da cewa:
"Bana son sayen jabon kaya, shin ku kuna son sayen kaya mara nagarta? Kun san waye Seyi Makinde kuma kun san abinda ya zuba maku tun lokacin da kuka damka amana a hannunsa a zaben 2019."
"Saboda haka, idan kuna son ci gaba da shan wannan romon hanya ɗaya ce ku ba shi damar ci gaba da ayyukan Alherin da ya fara."
"Ina mai amfani da wannan damar na fada maku baki daya, duk wani mai neman takara a inuwar sauran jam'iyyu, daga yau 5 ga watan Janairu, 2023, dan Allah ina rokon ku a karo na karshe, ku janye daga takara yanzun nan."
Zagi da hantara ba zasu girgiza ni ba - Wike
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Yi Bayani Kan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Marawa Baya a Zaben 2023
Alamu da ake iya gani a fili sun nuna cewa gwamna Wike ya yanke cewa ba zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ba a zabe mai zuwa.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa duk wanda ya zabi marawa baya, babu wani zagi ko sukar da zafa sanya ya janye daga kudirinsa.
Asali: Legit.ng