Tinubu Ya Dura Jihar Edo Edo Don Gudanar da Kamfen Jam'iyyar APC
- Jim kadan bayan kammala kamfen a jihar Kano, Bola Ahmad Tinubu ya shilla jihar Edo, zai gudanar da kamfen a can
- Tinubu ya samu tarbar jiga-jigan APC a jihar, kana yana tafe ne da manyan gwamnoni da jiga-jigan APC a kasar nan
- Ana ci gaba da kamfen yayin da ake ci gaba jiran kwanaki don gudanar babban zaben 2023 na shugaban kasa
Birnin Benin, jihar Edo - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya dura jihar Edo domin gudanar taron gangamin kamfen dinsa da kuma tallata muradansa.
An shirya gudanar gangamin kamfen na dan takarar shugaban kasan ne a yau Alhamis a filin wasa na Sam Ogbemudia da ke birnin Benin.
Vanguard ta ruwaito cewa, Tinubu na tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma na Jigawa, Abubakar Badaru da dai sauran jiga-jigan APC a wannan tafiyar.
Har ila yau, an ce ya samu tarbar gwamnan jihar Edo da mataimakin darakta janar na majalisar kamfen APC, Adams Oshiomole da manyan mambobi da jiga-jigan APC na jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya je Kano, ya cancare da rawa
Kafin tafiyarsa jihar Edo, dan takarar na jam'iyyar APC ya kai ziyara jihar Kano, inda ya bayyana kadan daga manufofinsa na gaje Buhari.
Wani rahoton da ya fito daga Kano ya ce, Bola Tinubu ya tika rawa a filin kamfen, inda ya bayyana farin cikinsa a bainar jama'a.
An ruwaito cewa, bayan ganin jama'a da yawa, Tinubu ya fara kwasar rawa ne don nuna irin dadin da ya ji da kuma yadda aka karrama shi a jihar ta Arewa.
Ana ci gaba da bayyana damuwa kan lafiyar Tinubu, wasu suna cewa ba shi da cikakkiyar laifyar da zai iya gudanar da mulkin Najeriya yadda ya ya dace.
Wallahi Tinubu ya fi ni koshin lafiya
A wani labarin kuma, abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima ya bayyana cewa, abokin nasa lafiyayye ne kuma zai iya mulkin Najeriya.
Shettima ya bayyana cewa, Tinubu ya fi shi cikakkiyar lafiya, don haka babu wani abin damuwa game da ba shi dama a bana.
Tun da aka ba Tinubu takarar shugaban kasa a APC ake ci gaba da kai ruwa rana kan batun da ya shafi lafiyarsa.
Asali: Legit.ng