2023: Zan Lallasa Zulum a Zabe Mai Zuwa, 'Yar Takarar Gwamnan Borno

2023: Zan Lallasa Zulum a Zabe Mai Zuwa, 'Yar Takarar Gwamnan Borno

  • Fatima Abubakar, 'yar takarar gwamna a jihar Borno karkashin jam'iyyar ADC ta lashi takobin lallasa Zulum a zaben 2023
  • 'Yar takarar ta bayyana yadda a koda yaushe take kara samun magoya baya da dumbun mabiya musamman mata saboda irin kamfen din gida-gida da ake
  • Haka zalika, ta musanta jita-jitan janyewa da ake yada tayi, saboda ba a ganin fostoci da banoninta kamar sauran 'yan takara

Borno - Fatima Abubakar, 'yar takarar gwamna a jam'iyyar ADC, ta lashi takobin lashe zaben gwamanoni a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa a jihar Borno.

Fatima, wacce ita ce kadai 'yar takarar gwamna mace a zabe mai karatowa ta bayyanawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya yadda ta fara kamfen din gida-gida don ta kai labari a zaben jihar.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, a cewarta, a kullum kara samun karbuwa da goyon baya gami da suna take yi daga jama'a, inda tace kusan tana da tabbacin lashe zaben.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

"A kullum kara suna da magoya baya nake, musamman mata wadanda suka yi amanna da cancanta ta wajen kawo canji da cigaba ga rayuwar mata da matasan jihar Borno.
"Zan so mata da matasan da muka tuntuba da su isar da sakon ga saura gami da bukatar gwada zaben tsirarun 'yan takara mata a zaben don kawo canji mai kyau."

- Cewar Ms Abubakar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

PM News ta bayyana cewa, ta musanta jita-jitan cewa ta janye daga gasar saboda ba a ganin fostocinta kamar na sauran, inda ta kara da cewa har yanzu akwai lokacin kamfen da zagaye.

"Muma muna shirye-shiryen namu zagayen."

- Cewar Ms Abubakar.

Yayin da ta bukaci zaman lafiya da isar da munufa a kamfen din, ta bukaci sauran 'yan takara da su aiwatar da nasu bisa ka'ida gami da girmama dokar zabe.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

"Ya kamata mu zama masu aiki don Borno ta fi haka, ba don son zuciya ba, kuma mu girmama ra'ayoyin mutane da zuciya daya."

- A cewarta.

NAN ta ruwaito yadda mata 16 ne kacal ke takara daga cikin 'yan takara 280 da zasu kara a gangamin zabe mai karatowa na 2023 a fadin kasar nan.

Tsabar hassada ke damun Obasanjo, Fadar Buhari tayi martani ga tsohon shugaban kasa

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi martani ga Cif Olusegun Obasanjo kan caccakar mulkin Buhari da yayi a sakonsa na sabuwar shekara.

Garba Shehu ya bayyana cewa, tsabar bakar hassada ce ta sa tsohon shugaban kasan ke sukar Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel