Obasanjo Ya Fi Tinubu, Buhari da Dukkan Jiga-Jigan APC a Hade, Inji Tsohon Dan Takarar Gwamnan Legas

Obasanjo Ya Fi Tinubu, Buhari da Dukkan Jiga-Jigan APC a Hade, Inji Tsohon Dan Takarar Gwamnan Legas

  • Tsohon dan takarar gwamna ya bayyana kadan daga alheran tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
  • Jigon na siyasa ya ce, Obasanjo ya fi Tinubu, Buhari da dukkan jiga-jigan APC a hade a komai da komai
  • Ana kai ruwa rana tsakanin jiga-jigan APC da kuma masu goyon bayan Peter Obi da Obasanjo a wannan makon

Jigon jam’iyyar Labour a jihar Legas, Babatunde Gbadamosi a ranar Takata ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki kan tabo toshon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

A makon nan ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, Tribune Online ta ruwaito.

Awanni bayan bayyana goyon bayansa ga Obi, tawagar kamfen ta APC ta ce Obasanjo ya ji kunya, kuma yana da rauni a fannin siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Bayan Obasanjo, Wani Babban Jigo a Najeriya Ya Sake Goyon Bayan Takarar Obi

Obasanjo ya fi Buhari alheri, inji jigon siyasan Kudu
Obasanjo Ya Fi Tinubu, Buhari da Dukkan Jiga-Jigan APC a Hade, Inji Tsohon Dan Takarar Gwamnan Legas | Hoto: newsdirect.com
Asali: UGC

A bangare guda, fadar shugaba Buhari ta caccaki Obasanjo, inda tace Buhari ya fi alheri ta kowane bangare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake martani, tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar ADP ya yi rubutu a Twitter, inda ya caccaki APC da fadar Buhari tare da cewa, Obasanjo ya fi kowa a jam’iyyar APC.

A cewarsa:

“Na ambata a 2019 cewa, girman karamar yatsar Obasanjo ta zarce ta Tinubu, Buhari da dukkan shugabannin APC idan aka gwama. Har yau dinnan gaskiya ne.”

Kishi suke da Obasanjo

Hakazalika, ya bayyana cewa, masu sukar Obasanjo ba don komai suke hakan ba sai don kishi da irin nasarori da ya samu na rayuwa.

A cewarsa, inda Obasanjo ya taka basu isa zuwa wurin ba, don haka suke hassada da karbuwarsa a idon duniya, News Direct ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

Daga karshe ya shaida cewa, ba laifi bane a ce mutum mai karimci kamar Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi ba, domin duk suna da mustawa mai kyau.

Gwamna Ortom ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi

A wani labarin kuma, gwamnan jam'iyyar PDP mai adawa da dan takarar jam'iyyarsu ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour.

Samuel Ortom ya sha bayyana adawa da Atiku da ma Fulani, inda yace jininsa ba zai taba haduwa da irinsu Atiku ba.

Gwamnoni biyar ne na PDP ke bayyana adawarsu ga Atiku, daya daga ciki dai ya fito ya bayyana wanda zai zaba a zaben bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.