Direktan Kamfen Din Matasa Na APC Ya Tafi Kan Dutse, Ya Yi Azumin Kwana 7 Da Addu'o'in Dare Don Nasarar Tinubu
- Honarabul Mike Msuaan ya fara azumin kwanaki bakwai da addu'o'i don nasarar Tinubu da Shettima a zaben shugaban kasa
- Ya yi kira ga yan Najeriya ba tare da la'akari da jam'iyya ba su taya shi addu'a su kuma zabi Ahmed Bola Tinubu a zaben mai zuwa
- Ya kara da cewa babu wani abu da ya rage illa ya mika komai ga hannun Ubangiji duba da cewa sauran kwana 25 zaben na Fabrairu
Ibadan - Gabanin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu, direktan tattara matasa na kwamitin kamfen dintakarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Hon. Mike Msuaan ya fara azumin kwana 7 kai tsaya tare da addu'oi a saman dutse saboda nasarar Tinubu-Shettima a zaben shugaban kasa.
A cikin sanarwa aka bawa Legit.ng jim kadan bayan dawowarsa daga addu'ar dare a wani dutse da aka yi a Ibadan, Hon. Msuaan ya ce babu abin da ya rage yanzu illa a mika komai a hannun Allah duba da cewa saura kwana 52 zaben.
Ya ce:
"Na yanke shawarar in koma ga Ubangiji na yi azumin kwana 7 kai tsaye da addu'o'i ga Ubangiji ya bamu shugaban da muke so wanda zai sauya kasarmu. Babu abinda Allah ba zai iya yi ba. Kamar yadda na hau kuma na sauka daga duwatsu masu tsarki, na yi imanin Allah zai amsa addu'a ta da addu'ar mutanen kirki a kasar mu ya bamu shugaba kamar Annabu Dauda."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Direktan, ya kuma yi kira ga sauran yan Najeriya ba tare da la'akari da jam'iyya ba su taya shi addu'a kuma su zabi Sanata Ahmed Bola Tinubu a zaben don nasara.
Hon. Mike Msuaan, daga nan ya bayyana alherin da aka samu a gwamnatin APC mai ci a yanzu kuma ya ce ya kamata a tabbatar alherin ya dore ta hanyar zaben wanda zai iya cigaba daga inda Shugaba Buhari ya tsaya.
Gwamnan Ondo ya ce APC ne za ta mulki Najeriya shekaru 8 masu zuwa
A wani rahoton, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce jam'iyyar APC ne za ta cigaba da mulkar kasar na shekaru takwas nan gaba.
Jigon na APC ya zama dole a cigaba da fafutikan ganin kudancin kasar ta samar da shugaban kasa, duba da cewa arewa ta yi shekara takwas tana mulki.
Asali: Legit.ng