2023: Abin da ya sa Mu ka Tsaida Bola Tinubu a Jam’iyyar APC Inji Sanatan Arewa

2023: Abin da ya sa Mu ka Tsaida Bola Tinubu a Jam’iyyar APC Inji Sanatan Arewa

  • Aliyu Magatakarda Wamakko ya hadu da kabilu dabam-dabam yayin da ya je gidansa a garin Sokoto
  • Tsohon Gwamnan ya ce kokarin ganin an samu hadin-kai ya sa Bola Tinubu ya samu tikitin Jam’iyyar APC
  • Sanatan na jihar Sokoto ya nuna irin yunkurin da ya yi a gwamnatinsa na ganin an zauna lafiya da juna

Sokoto - Jagora a jam’iyyar APC kuma Sanata mai-ci, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya yi bayani a kan dalilin bada takarar 2023 ga Asiwaju Bola Tinubu.

Tribune ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba 2022, ta ce Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi karin hasken nan ne a gidansa.

Da yake magana a gaban majalisar Sarakuna a gidansa da ke Gawon Nama a garin Sokoto, tsohon gwamnan ya yi maraba da wadanda suka kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

2023: Ta Karewa Atiku, Darakta Janar Na Kwamitin Kamfen PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Sanata Aliyu Wamakko yake cewa Sokoto tana maraba da kowane mutum ba tare da yin la’akari da kabilarsa ko yankin da ya fito daga duk fadin kasar nan ba.

Zaman lafiya ake nema

‘Dan majalisar ya ce saboda ganin zaman lafiya da hadin-kai ya wanzuna tsakanin al’umma, shiyasa aka tsaida Tinubu ya zama ‘dan takarar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Najeriya kasar mu ce gaba daya, shiyasa ake bukatar mu hada-kai, domin makomarmu tayi kyau.

- Aliyu Magatakarda Wamakko

Bola Tinubu
'Dan takaran APC a 2023, Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

An rahoto Wammako yana cewa a lokacinsa ne gwamnatin Sokoto ta soke kudin karatu da mutanen da ba asalin ‘yan jihar ba suke biya a manyan makarantu.

Bugu da kari, tsohon Gwamnan ya ce ya dauki bare daga wata jiha, ya nada shi a matsayin Mai ba shi shawara, saboda kurum sauran jama’a su ji ana yi da su.

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

Alwashin Aliyu Magatakarda Wamakko

A nan ne ‘dan siyasar ya yi alkawari ga Sarakunan cewa jam’iyyar APC za ta kula da su, idan dai mutane suka zabe ta, ta koma kan karagar mulki a zaben bana.

Punch ta ce Surajudeen Sahabi ya gabatar da jawabi a madadin sauran sarakan, ya sanar da Sanatan cewa a shirye suke da su taimakawa nasarar APC a zabe.

A wajen zaman da aka yi, kabilu kamar Yarbawa, Ibo, Tiv da Hausa sun aika wakilan da suka gabatar da jawabi domin a nuna hadin-kan da ake da shi a kasar.

Hasashen zaben 2023

An ji labari cewa hasashe ya nuna za a gwabza tsakanin Jam’iyyar APC, PDP da kuma NNPP a Jihohin Arewa, amma ba a maganar Peter Obi da LP a yankin.

A irinsu Enugu, Ebonyi, Imo, Abia da Anambra, Obi ake ba nasara, Bola Tinubu zai iya karbe duka Jihohin Yarbawa. Watakila sai zaben ya kai zuwa zagaye na biyu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng