Gwamna Umahi Na APC Ya Musanta Jita-Jitar Cewa Yana Koma Bayan PDP
- Gwamna Umahi na jam'iyyar APC ya ce maganar yana goyon bayan dan takarar PDP a zabe mai zuwa karya ne
- Gwamnan wanda ke neman takarar Sanatan Ebonyi ta kudu a inuwar APC, yace jita-jitar ba ta kama hanyar gaskiya ba ko kadan
- David Umahi ya roki masu fada aji daga kowane bangare da su rungumi tsarin karba-karba a mulkin jihar dake kudu maso gabas
Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa yana goyon bayan dan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyar PDP, Ifeanyi Chukwuma a zaben 2023.
Jaridar Daily Nigerian tace Umahi ya musanta jita-jitar ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan Midiya, Chooks Oko, ya fitar a Abakaliki, baban birnin Ebonyi.
Mista Oko yace gwamnan ya yi karin haske kan lamarin ne a mahaifarsa Uburu, karamar hukumar Ohaozara, lokacin da ya karɓi bakuncin kungiyar Kiristoci CAN.
Gwamna Umahi, dan takarar Sanatan Ebonyi ta kudu karkashin inuwar APC, ya ce jita-jitar ba ta yi kama da gaskiya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Masu cewa Odili wani kaya ne a hannun mu sun tafka kuskure, da ace sun san kalubale da farmakin da ake kawo mun a kowace rana da ba zasu fadi haka ba."
"Inda zan goyi bayan wani ɗan takara, to da wani daban zan karkata a kai wanda ya hito daga karamar mazaba amma ba mutumin da ya fito daga shiyyar da nake ba."
Ya kamata kowa ya rungumi tsarin karba-karba - Umahi
Gwamnan ya roki CAN, dattawa da iyaye da masu ruwa da tsaki a jihar Ebonyi da su goyi bayan tsarin karba-karba domin samun ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali.
"Lokacin da muke neman takara a 2023, yan shiyyar arewa ta tsakiya sun mara mana baya, shugabannin su sun tsaya kan a zabe mu," inji Umahi.
A wani labarin kuma Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003
Alaka na kara tsami tsakanin Atiku Abubakar da Wike, hadimin dan takarar shugaban kasa na PDP ya dirararwa gwamna Ribas kan asirin da ya tono. Wike dai yace a 2003, sai da Obasanjo ya duka kan guiwa ya roki Atiku ya bari ya nemi tazarce amma duk da haka sai da ya gindaya masa sharudda.
Asali: Legit.ng