2023: Abokin Takarar Atiku Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Wike Ya Masa Zazzafan Martani

2023: Abokin Takarar Atiku Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Wike Ya Masa Zazzafan Martani

  • Gwamnan jihar Ribas kuma jagoran G-5 a jam'iyyar PDP ya maida martani kan kalaman Allah ke ba da mulki ba G5 ba
  • Nyesom Wike yace tawagarsa ba su taba wasa da karfin ikon Allah ba, amma yan Najeriya su sani Allah ba zai ba mugu mulki ba
  • Ana ta musayar yawu tsakanin kusoshin PDP tun bayan da Wike yace a watan Janairu zai fadi inda ya dosa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa shi da abokansa na G-5 basu taba gigin wasa da karfin ikon Allah na baiwa wanda ya so mulkin Najeriya ba.

Leadership tace gwamnan ya faɗi haka ne a matsayin martani ga wasu kalamai da aka ce gwamnonin G-5 ba su isa su zabi shugaban kasa na gaba ba a Najeriya.

Gwamna Wike.
2023: Abokin Takarar Atiku Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Wike Ya Masa Zazzafan Martani Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya yi martanin ne a wurin kaddamar da fara aikin Titin Ogbo zuwa Ihugbodo, karamar hukumar Ahoada ta gabas da ke jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi

Yace duk da Allah ke ba da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, amma ba zai miƙa mulki ga mugayen mutane ko sheɗanu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Wike ya ce:

"Kar ka bari duniya ta yaudare ka saboda kana son mulki, Allah ba zai zakulo mugun mutum ya ba shi mulki ba. Hannayen mu tas suke ba mu yi wani abu na kuskure ba."
"Duk abun mai sauki ne domin abinda muke fafutuka shi ne a yi abinda kowa zai ji ana tafiya da shi, wanda kowanen mu zai ji a ransa kanmu a haɗe yake."

Gwamna Wike ya kara da bayanin cewa mambobin tawagar gaskiya watau G-5 sun yi imani da karfin ikon Allah shi kadai kuma haka ya sanya kullum suke kara karfi.

Babu rabuwar kai a G-5 inji Wike

Kara karanta wannan

Baraka ta Kunno G5, Wike Ya Fusata da Gwamnonin PDP kan Wanda Za a Marawa Baya

Bugu da kari, gwamnan Ribas ya bayyana cewa wanda ya yi ikirarin cewa kawunan mambobin G5 ba a haɗe yake ba, ya sani wannan jita-jitar an jima da binne ta.

Vanguard ta rahoto Wike na cewa:

"Bai yi tasiri ba kuma da ikon Allah ba zata yi tasiri ba, wani ya zauna ya kirkiro cewa akwai rabuwar kai, ina maka fatan da kake mana."

A wani labarin kuma Gwamna Obaseki yace ya shirye yake ya sa Cacar kudi kan cewa APC ba zata tabuka komai ba a zaben 2023

Gwamna Godwin Obaseki yace ko rantsuwa ya yi ba zai kaffara ba mutane sun gaji da mulkin APC, ba zasu sake zabenta ba a zabe mai zuwa.

A cewarsa kaso 25 cikin 100 da ake son jam'iyya ta hada a kowace jiha, APC ba zata samu ba a jiharsa ta Edo a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: Tashin hankali yayin da wani Alhaji ya mutu yayin bin layin gidan mai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262