Wani Mai Mota a Oyo Ya Yanki Jiki Fa Fadi, Ya Mutu a Layin Gidan Mai

Wani Mai Mota a Oyo Ya Yanki Jiki Fa Fadi, Ya Mutu a Layin Gidan Mai

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wani Alhaji ya mutu a wani gidan mai a jihar Oyo a Kudu maso Yamma
  • An tattaro cewa, wannan lamari ya ba da mamaki lokacin da aka gano mutumin ya mutu yana bin layin mai
  • Ba a samu jin karin bayani ta bakin rundunar ‘yan sanda ba, amma majiya ta tabbatar da faruwar lamarin

Jihar Oyo - Wani mai motan da ya zuwa yanzu ba a bayyana sunansa ya mutu a Oluyole Estate da ke karamar hukumar Oluyole a jihar Oyo yayin da yake bin layin siyan man fetur a gidan man yankin.

Wannan lamari mai taba zuciya ya faru ne a ranar Talata 27 ga watan Disamba, inji rahoton jaridar Punch.

An tattaro cewa, babu wanda yasan cewa mutumin ya mutu a lokacin da ya daura kansa a kan matukin motar yayin da yake jiran isowar layinsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Mai mota ya mutu a layin siyan mai
Wani Mai Mota a Oyo Ya Yanki Jiki Fa Fadi, Ya Mutu a Layin Gidan Mai | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Lokacin da sauran jama’a suka fara danna ham din motocinsu kan ya ja layi gaba, nan ne aka gane tuni ya mutu ba ya motsi kwata-kwata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattara gawarsa zuwa wani wuri

Tuni aka dauke motar mai lamba AKD 878 GP zuwa ofishin ‘yan sanda, kana aka dauke gawar zuwa wurin ajiye da ba a bayyana ba.

A cewar wata majiya:

“Ba a bayyana wanene mutumin ba har yanzu. Ya yi kama da wani Alhaji dai haka kuma yana zaune a motarsa kafarsa daya a kan feda daya kuma a waje tare da kofar motar a bude.”

Manajan gidan man, wanda aka bayyana da Mr Joseph ya ce, wannan lamari dai tuni ya je gaban ‘yan sanda kuma an dauke gawar mamacin, Within Nigeria ta tattaro.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, Adewale Osifeso.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin hadimar gwamna a jihar Legas

Najeriya na yawan fama da karanci man fetur, musamman a wannan shekara ta 2022, inda farashin mai ya zama kamar na gwal.

An yi rabon jarakunan man fetur a gidan biki a madadin kayan zugege da baki za su koma dashi gida.

Wannan lamari ya tada hankali, mutane da yawa a ciki da wajen Najeriya ne suka yi da martani a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel