2023: Za Mu Kawo Wa Atiku Kuri’u Miliyan 1 – Yan Najeriya a Turai Sun Dauki Alkawari
- Atiku Abubakar ya samu goyon bayan wasu yan Najeriya da ke zaune a Turai gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023
- Mazauna kasar wajen sun ce suna goyon bayan tsohon maaimakin shugaban kasar ne saboda gogewarsa a harkar shugabanci
- Kungiyar ta bukaci yan Najeriya a gida da waje da kada su manta da alakar siyasa sannan su marawa takarar shugabancin Atiku/Okowa baya gabannin zaben
Abuja - wata kungiyar fitattun yan Najeriya mazauna Turai karkashin inuwar 'Nigerian Professionals for Atiku Abubakar in Europe' sun yi alkawarin kawowa dan takarar shugaban kasana jam'iyyar PDP akalla kuri'u miliyan daya a zaben 2023 mai zuwa.
Kungiyar ta ce tana muradin ganin kasar ya samu tsaro, ci gaban tattalin arziki da rayuwa mai inganci ga kowa, don haka akwai bukatar goyon bayan shugaba mai tarin gogewa wanda ya shirya ma hakan a cikin sauran yan takarar shugaban kasar, rahoton Leadership.
A cikin waa sanarwa da aka aikewa Legit.ng a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba, dauke da sa hannun jagoranta a Turai, Collins Osazee Idahosa, kungiyar ta ce ta nada jagorori 23 a fadin kasashe daban-daban a nahiyar Turai a kokarinta na cimma nufinta.
Jerin sunayen nade-naden da kungiyar ta yi
Ya ce wasu daga cikin jagororin sun hada da; Bridget Omoregie na Ireland, Roland Edomwonyi na Sweden, Sylvester Idahosa na Spain, Osariemen Erhabor na Finland, Solomon Obazeena Ingila, Alex Okitikpi na Faransa, Austin Osiomofo na Belgium da Queen Aghibe na Cyprus.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, kungiyar ta nada King Nelson a kasar Jamus da Helen Osas Okhuarobo a Italiya da dau sauransu.
Kungiyar ta kuma yi amfani da damar wajen godiya ga dukkan jagororin a kan sadaukarwa da suka yi sannan ta yi masu fatan shiga shekarar 2023 cikin wadata yayin da ta yiwa Najeriya da yan Najeriya na gida da waje addu'an jin dadin wannan sabuwar shekara cikin albarka.
Idahosa ya kuma bukaci yan Najeriya mazauna gida da waje da kada su manta da alakar siyasa sannan su hango makomarsu a tafiyar Atiku/Okowa, rahoton Nigerian Tribune.
Wani bangare na jawabin na cewa:
"Kungiyar 'Nigerian Professionals for Atiku Abubakar Europe' kungiya ce ta duniya da jagorori 23 a fadin kasashen Turai daban-daban.
"Mun yi alkawarin kawowa Atiku kuri'u miliyan daya sannan mu maimaita abun da muka yi a zaben gwamnan jihar Osun na karshe a kan Atiku da jam'iyyar People's Democratic Party."
Atiku ya gana da gwamnonin APC a cikin sirri, Wike
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da yin zawarcin wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC.
A cewar Wike, Atiku ya sa labule cikin sirri da wasu gwamnonin jam'iyyar mai mulki a kasar Dubai.
Asali: Legit.ng