Tinubu Ne Zai Maida Najeriya Ta Zama Sabuwa, Inji Jam’iyyar APC Mai Mulki

Tinubu Ne Zai Maida Najeriya Ta Zama Sabuwa, Inji Jam’iyyar APC Mai Mulki

  • Jam’iyyar APC ta ce Tinubu ne zai iya kawo ci gaba a Najeriya aka zabe shi ya gaji shugaba Muhammadu Buhari
  • A cewar mataimakin shugaban jam’iyyar, Tinubu zai ci gaba da ayyukan da Buhari ya fara a mulkinsa
  • ‘Yan takara da magoya bayansu na ci gaba da tallata kansu gabanin zaben 2023 mai zuwa ga mai rabon gani

Najeriya - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief Emma Eneukwu ya bukaci ‘yan Najeriya da su bi tafarkin nasara ta hanyar goyawa dan takarar jam’iyyar, Bola Tinubu a zaben 2023.

Ya bayyana cewa, Tinubu ne zai samar da sabuwar Najeriya ta hanyar daurawa daga inda Buhari ya tsaya a zaben 2023.

Ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a wani sakon sabuwa shekara, inda yace Tinubu a shirye yake ya mulki Najeriya ta hanyoyin da za su kawo ci gaba, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Ɗau Dumi, Yace Zai Zuba Dukiyarsa a Caca Kan APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'u Ba a 2023

Tinubu ne zai iya gyara Najeriya, inji APC
Tinubu Ne Zai Maida Najeriya Ta Zama Sabuwa, Inji Jam’iyyar APC Mai Mulki | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

'Yan Najeriya na bukatar shugaba kamar Tinubu

A cewarsa, ‘yan Najeriya na bukatat shugaban da yake da tarihin kwarewa kuma wanda zai yi tafiya da kowa ya kuma gina daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa, Tinubu ya nunawa ‘ya Najeriya abubuwan da zai musu a cikin takardar manufansa, kuma zabansa zai yiwa ‘yan kasar amfani ainun.

Eneukwu ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji sauraran maganganun karya masu kushe dan takarar da zai cire su daga kangin wahala.

Tinubu zai sauya Najeriya ta zama sabuwa

A cewarsa, Tinubu ya nuna kansa a matsayin shugaban da zai ciyar da Najeriya gaba idan ya samu dama, rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN).

A kalamansa:

“Za mu sabuwar Najeriya ne kawai idan muka goyi bayan APC ta ci gaba; domin ta kammala ayyuka da shirye-shiryen da aka fara.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abin Kunya Ne Buhari Ya Mika Mulki Ga Yan Adawa, In Ji Abdullahi Adamu

Hakazalika, ya ce kada ‘yan Najeriya su bari wannan dama ta wuce musu, don haka su zabi Tinubu a zaben 2023.

Daga karshe, ya bayyana bacin ransa ga yadda wasu tsageru ke kone ofisoshin hukumar zaben mai kanta, INEC a wasu yankunan Kudancin kasar nan.

Da fari kun ji cewa, Tinubu ne dan takarar shugaban kasan da 'yan Najeriya suka fi neman bayanansa a kafar Google a shekarar 2022, daga shi sai Peter, Atiku da dai sauran 'yan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.