Bola Tinubu Ne ’Yan Najeriya Suka Fi Neman Bayansa a Kafar Google a Shekarar Nan a 2022

Bola Tinubu Ne ’Yan Najeriya Suka Fi Neman Bayansa a Kafar Google a Shekarar Nan a 2022

  • Dan takarar shugaban kasa a APC ne ya fi zama sananne a jerin ‘yan takarar da aka fi nema a kafar Google
  • Peter Obi ya zo na biyu Atiku kuwa ya zo na uku a jerin ‘yan takarar da suka fito a Najeriya a zaben 2023
  • Ana ci gaba da jiran zaben 2023 mai zuwa, ‘yan Najeriya na ci gaba da shirin zaban dan takarar da suke so

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne ya fi sanuwa a kafar nema ta Google a jerin ‘yan takarar shugaban kasa a badi.

Kafar nema ta Google na tattara bayanai kan abin da mutane suka fi ra’ayi a kai da kuma nuna sha’awa a duk wata, na karshe a shekarar nan shine na 30 ga Nuwamba zuwa 27 ga Disamba.

Kara karanta wannan

Yadda Bola Tinubu Ya Kawo Karshen Mummunan Rikicin Jam’iyyar APC Cikin Ruwan Sanyi

A binciken da aka yi, daga watan Fabrairun 2022 ya nuna yadda ake neman bayanai game da ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa, PM News ta ruwaito.

Tinubu ne ya fi sanuwa a 2022 a kafar Google
Bola Tinubu Ne ’Yan Najeriya Suka Fi Neman Bayansa a Kafar Google a Shekarar Nan a 2022 | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Adadin kason nema na ‘yan takarar shugaban kasa

Kididdigar Google Trends ta nuna cewa, Tinubu ya samu kaso 43% na sha’awar nema a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ne ya zo na biyu tare da kaso 28% a kafar neman ta Google.

Na uku a jerin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya sami kaso 26% a jerin ‘yan takarar.

Kwankwaso da sauran ‘yan takara

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ne yake da kaso 3% a jerin ‘yan takarar, rahoton Blueprint.

Kara karanta wannan

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Sauran wadanda suke cikin jerin sun hada da farfesa Christopher Imumolen na jam’iyyar Accord, Osita Nnadi na jam’iyyar APP, Kolawole Abiola na jam’iyyar PRP da kuma Yabaji Sani na jam’iyyar ADP dake da 0% a jerin.

Hakazalika, akwai Ado-Ibrahim Abdulmalik na jam’iyyar YPP Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, Mamman Dantalle, Chukwudi Umeadi, Olufemi Adenuga da dai sauransu da suka samu -1%.

A wani labarin kuma, Tinubu ya ce bai gana da wasu gwamnonin PDP ba a Landan, don haka an kirkiri labarin ne don yada karya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.