Ganduje Bai Kore Ni Ba, Da Kaina Na Ajiye Aiki, Ina da Shaidan Hakan, Inji Tsohon Kwamisha Baba Impossible

Ganduje Bai Kore Ni Ba, Da Kaina Na Ajiye Aiki, Ina da Shaidan Hakan, Inji Tsohon Kwamisha Baba Impossible

  • Tsohon kwamishina a jihar Kano ya bayyana gaskiyar abin da ya faru, ya ce ba wanda ya koreshi daga aiki
  • Baba Impossible ya ce da kansa ya yi niyyar ajiye aiki, kuma yana da shaidan hakan a hannunsa da kwafin gwamnati
  • Gwamnatin Kano ta ce da kanta ta kori Baba Impossible, ta ce ba ya biyayya ga ka'idojin aiki gwamnati

Jihar Kano - Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya ce ba gaskiya bane labarin da ake cewa gwamna Ganduje ya kore shi daga mukamin kwamishinan addinai na jihar Kano.

Baba Impossible ya ce, shi ya yi radin kansa ya ajiye aikinsa sabanin zaton cewa an kore shi.

Ya bayyana wannan batu ne a wata tattaunawa da ya yi wa BBC Hausa, inda yace ya ba da takardar ajiye aikinsa tun a ranar 30 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamna Ganduje Ya Kori Kwamishinan Addinai Daga Aiki Kan Wasu Dalilai

Ba Ganduje bane ya kore, ni ajiye aiki, inji Baba Impossible
Ganduje Bai Kore Ni Ba, Da Kaina Na Ajiye Aiki, Ina da Shaidan Hakan, Inji Tsohon Kwamisha Baba Impossible | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewarsa, tuni an karbi takardar, aka buga mata hatimi tare da ba shi kwafin takardar don ajiye a gaba, ya kuma bayyana cewa, bai fadi dalilin ajiye aikinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganduje ne ya kori Baba Impossible

A bangare guda, wata sanarwa da kwamishinan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar ta ce, gwamna ganduje ne ya bayyana korar Baba Impossible.

Hakazalika, sanarwar ta ce, Dr. Nazifi Bichi ne aka bayar don maye gurbin Baba Impossible.

A cewar sanarwar, an kori Baba Impossible ne saboda rashin da’a a ka’idan aikinsa da kuma saba tsarin aikin gwamnati.

Hakazalika, kwamishinan ya ce ana zargin Baba Impossible da rashin yiwa gwamnati rashin biyayya.

Tinubu na kaunar 'yan Arewa, ya kamata su zabe shi a zaben 2023 mai zuwa

A wani labarin kuma, mai girma gwamna Ganduje ya ce 'yan Arewa ba su da zabin da wuce su zabi dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Ganduje ya bayyana cewa, Tinubu ya taimakawa 'yan Arewa wajen kafuwar dimokradiyya kuma kasar nan ta shaida tasirinsa.

A cewar Ganduje:

"Arewa da yan arewa ba su da uzuri illa su goyi bayan Tinubu kuma su zabi jam'iyyar APC. Bola Ahmed Tinubu ya daka rawar gani sosai yayin da kuma ya taimakawa yan arewa da cigaban Najeriya. Don haka, lokacin sakayya ya yi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.