Gwamna Ganduje Ya Kori Kwamishina Kan Kalamai Marasa Kan Gado

Gwamna Ganduje Ya Kori Kwamishina Kan Kalamai Marasa Kan Gado

  • Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tunbuke kwamishinan harkokin Addinai, Dr Muhammad Tahar Adam daga mukaminsa
  • A wata sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar ranar Jumu'a tacr an ɗauki matakin ne saboda rashin ɗa'a da nuna isa
  • Ganduje ya gode masa tare da yi masa fatan Alheri a harkokin da zai tasa nan gaba

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kori kwamishinan kula da harkokin addinai, Dakta Muhammad Tahar Adam.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ana zargin kwamishinan da kalaman rashin ɗa'a marasa kan gado kuma yana tafiyar da harkokin ofishinsa kamar kasuwanci.

Gwamna Abdullahi Ganduje.
Gwamna Ganduje Ya Kori Kwamishina Kan Kalamai Marasa Kan Gado Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Kano, Mallam Muhammad Garba, ya fitar ranar Jumu'a yace matakin korar ta fara aiki ne nan take.

Ganduje ya tura sunan wanda zai maye gurbinsa majalisa

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Garba ya kara da cewa tuni gwamna Ganduje ya aika da sunan wanda ya zaɓa, Dakta Nazifi Ishaq Bichi na jami'ar Bayero da ke Kano zuwa majalisar dokoki domin maye gurbinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace an yanke shawarin korar kwamishinan ne sakamakon wasu halayr marasa kyau da kuma maganganu marasa kan gado da ya rika yi a matsayinsa na mai rike da babban Ofis.

Dalilin da yasa Ganduje ya kori kwamishina

A cewar Mista Garba, tsohon kwamoshinan wanda ya fi shahara da 'Baba Impossible' an gano yana, "tafiyar da harkokin Ofishinsa kamar kasuwanci, yana rage wa ma'aikata kwanakin aiki."

Kwamishinan yaɗa labarai ya ƙara da cewa ba ya ga tafiyar da harkoki ba tare da neman izini ba, Baba Impossible ya zama mai kunnen ƙashi ba ya wa gwamnati biyayya.

Daga karshe, Sanarwan tace mai girma gwamna ya yi wa korarren kwamishina fatan Alheri da dukkan abubuwan da ya sa gaba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Sabunta Nadin Wani Mukamin Gwamnati Mai Muhimmanci

A wani labarin kuma Gwamna Okowa yace gwamnatin Atiku zata fatattaki yunwa, Talauci da rashin tsaro idan aka zabi PDP a 2023

Yace gwamnatin jam'iyyar APC da ke mulki yanzu haka ta maida hannun agogo baya na tsawon shekaru da wannan mulkin na ta na kama karya.

A cewar Okowa, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP lokaci ya yi da 'yan Najeriya zasu farka daga bacci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel