Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

  • Allah ya yi wa shugaban jami'ar Achiever da ke Owo, Farfesa Samuel Aje, rasuwa ranar.Alhamis 29 ga watan Disamba 2022
  • Bayanai sun nuna cewa VC ya tafi hutun bukukuwan Kirsimeti zuwa Legas lafiyarsa kalau amma sai labarin mutuwarsa ta fito Alhamis da safe
  • Jami'in hulda da jama'a na jami'ar ya tabbatar da lamarin amma yace suna jiran smaun bayani ne kan musabbabin mutuwar

Ondo - Shugaban Jami'ar Achievers da ke Owo, jihar Ondo, Farfesa Samuel Aje, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa shugaban jami'ar ya tafi jihar Legas domin shagalin bikin kirsimeti ranar Jumu'a ta makon da ya gabata kuma ya rasu ne da safiyar Alhamis 29 ga watan Disamba, 2022.

Samuel Aje.
Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Har zuwa yanzun da muke haɗa maku wannan rahoton babu wani bayani sahihi kan musabbabin abinda ya yi ajalin Marigayi VC, wanda ya shiga Ofis tun a watan Yuni, 2020.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnan APC Ya Ce Kudu Za Ta Shugabanci Najeriya Shekaru 8 Masu Zuwa

Da yake tabbatar da mutuwar, shugaban sashin hulda da jama'a na Jami'ar Achirvers, Mista Adebayo Olagunju, ya ce har yanzun hukumar makaranta na dakon jin abinda ya yi ajalin VC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ayyana mutuwar Farfesa Aje ba zato ba tsammani da, "abun takaicin da ake gudu," kuma ya kara da cewa kafatanin jami'ar ta kaɗu lokacin da labarin ya watsu.

"Nan ba da jimawa ba iyalansa za su fitar da cikakken bayani kan abinda ya faru," inji Olagumju.

Wani babban Malami a jami'ar wanda ya yi jawabi bisa sharadin boye bayanansa ya ce rasuwar VC ta kaɗa su kuma sun sgiga damauwa.

"Mun kaɗu sosai lokacin da muka samu labarin rasuwarsa, ba bu wata alamar rashin lafiya a jikinsa kafin tafiya hutun Kirsimeti amma har yanzu bamu san me ya yi ajalinsa ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PSC ta Dakatar da Jami’in da Ya Harbe Lauya Mai Ciki a Legas

Tsohon Sanatan PDP ya kwanta dama

A wani labarin kuma Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Sanatan PDP Ya Mutu a Asibitin Abuja

Inatimi Spiff, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Bayelsa ta Gabas a majalisar dattawa, ya mutu ne ranar Asabar, 24 ga watan Disamba, a asibitin Abuja bayan dan gajeruwar rashin lafiya.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta ce mutuwar Sanata Spiff ya jefa jam'iyyar cikin bakin ciki da alhini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel