Ta Kwaɓe Wa Dogara Yayin Da Shugabanin Kirista Da Yan Uwansa Suka Goyi Bayan Tikitin Musulmi-Musulmi Na Tinubu
- Tafiyar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta sake samun babban tagomashi
- Hakan na zuwa ne yayin da magoya bayan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, suka goyi bayan Tinubu duk da tikitin musulmi-musulmi
- Kungiyar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda ayyukan alheri da Tinubu ya yi a Legas, tana mai cewa za ta tattaro masa kuri'un yan karkara
Daruruwan yan yankin su tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, suna cewa tikitin musulmi-musulmi bai kamata ya zama dalili ba a zaben na 2023.
Dogara, wanda ke wakiltar yankunan Dass/Tafawa Balewa/Bogoro a jihar Bauchi, yana daga cikin yan gaba-gaba wurin sukar tikitin musulmi-musulmi na APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan garinsu Dogara sun juya masa baya
Saboda rashin gamsuwa da matakin jam'iyyar, Dogara ya fita daga APC ya koma PDP, inda ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, Atiku Abubakar, The Times ta rahoto.
Amma, yan yankinsu daga kananan hukumomi uku na Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, sun yi ralli don nuna goyon bayansu ga Tinubu da Shettima, da dan takarar gwamna na APC, Sadique Abubakar da wasu yan takarar APC.
Abin da yasa muka yi watsi da Dogara, shugabannin kirista sun bayyana dalili
Magoya bayan, karkashin kungiyar 'Bogoro, Dass and Tafawa Balewa Christian Support Group for APC' sun ce sun yi ralli ne don fada wa dan takarar shugaban kasarsu da jam'iyyar cewa za su tafi gida-gida don yin kamfen gabannin babban zaben.
Da ya ke magana wurin taron, daya cikin wadanda suka shirya taron kuma tsohon mai neman takarar yankin Dass/Tafawa Balewa/Bogoro, Dr Godfrey Manasseh, ya ce sun yanke shawarar goyon bayan Tinubu ne saboda nasarorin da ya samu a jihar Legas lokacin yana gwamna, Punch ta rahoto.
Manyan yan APC da ke adawa da tikitin musulmi da musulmi na Tinubu a 2023
A gefe guda, a watan Yuli na shekarar 2022 ne dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya zabi Sanata Kashim Shettima matsayin matsayin wanda zai masa mataimaki.
Amma, wannan zabin nasa ya janyo cece-kuce a kasa da ma jam'iyyar ta APC inda wasu ke ganin ba a yi wa kiristocin arewa adalci ba kuma hakan na iya raba kasa.
Asali: Legit.ng