2023: An Yi Mamaki Yayin Da Sanatan PDP Mai Tasiri Ya Bukaci Matasa Su Zabi Tinubu, Ya Bada Kwakwaran Dalili

2023: An Yi Mamaki Yayin Da Sanatan PDP Mai Tasiri Ya Bukaci Matasa Su Zabi Tinubu, Ya Bada Kwakwaran Dalili

  • Tafiyar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta sake samun babban tagomashi
  • Wannan na baya-bayan na zuwa ne daga sanata mai wakiltan Enugu East, Chimaroke Nnamani, wanda ya yi kira ga matasa su yi wa Tinubu kamfen kuma su zabe shi a zaben 2023
  • A cewar sanatan na PDP, tsohon gwamnan na jihar Legas ya taka rawar gani a siyasa kuma ya cancanci a bashi goyon baya ya ci zaben shugaban kasa

Sanata mai wakiltar Enugu East, Chimaroke Nnamani, ya bukaci matasan Najeriya su zabi dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana mai cewa yana da tsare-tsare masu kyau ga matasa.

Nnamani, sanata a karkashin jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya nuna cewa yana da basirar bullo da tsare-tsare da za su amfani matasa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

Bola Tinubu
2023: An Yi Mamaki Yayin Da Sanatan PDP Mai Tasiri Ya Bukaci Matasa Su Zabi Tinubu, Ya Bada Dalili. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Chimaroke ya bada dalilin da yasa ya kamata matasa su zabi Tinubu

Sanatan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba ya ce tunda Tinubu ya shiga ofis a 1999, ya rika bullo da tsare-tsare don magance rashin ayyukan yi, rashin tsaro da ke damun matasa.

Ya ce a lokacin matasa na tururuwa zuwa Legas don neman arziki, ya kara da cewa Tinubu ya fahimci hakan kuma da matasan sun zama fitina ga jihar idan ba a tanadi tsare-tsaren inganta tattalin arziki ba ga ayyuka gare su.

A cewarsa, dan takarar shugaban kasar na APC ya kafa shirin yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi don wayar da kan matasa hadarin da ke tattare da kwaye.

Sanatan ya ce:

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

"Domin magance kalubalen, Tinubu ya raba jari na fiye da miliyan daya ga kungiyoyin matasa da suka yi rajista a matsayin tukwici saboda hadin kansu wurin karfafa masu gwiwa.
"Gwamnatin Tinubu ta kafa cibiyoyin koyon sana'o'i a Maris din 2003 don sauya tarbiyan yan daba, masu zaman kashe wando, da masu kwana a titi da ke fatan sauya rayuwarsu inda aka koyar da su sana'o'i kamar kafinta, kera takalma, gyaran kai da rini."

Nnamani shine gwamnan jihar Enugu daga shekarar 1999 zuwa 2007, lokacin Tinubu yana gwamna a Legas.

2023: Twist as Powerful PDP Senator Asks Youths to Vote for Tinubu, Gives Strong Reason

2023: An Yi Mamaki Yayin Da Sanatan PDP Mai Tasiri Ya Bukaci Matasa Su Zabi Tinubu, Ya Bada Dalili

Zaben 2023: Yan garinsu Dogara sun juya masa baya, sun goyi bayan Tinubu

2023: Ta Kwabe Wa Dogara Yayin Da Shugabannin Kirista Da Yan Uwansa Suka Goyi Bayan Tikitin Musulmi-Musulmi Na Tinubu

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Dau Alkawarin Gina Masallaci da Coci a Wani Kauye

Yan garinsu Dogara sun juya masa baya, sun koma bangaren Asiwaju Bola Tinubu

Daruruwan al'umma daga yankin da tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Yakubu Dogara ya fito, sun fito sun bayyana goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Sun ce sun yanke shawarar goyon bayan dan takarar shugaban kasar na APC ne saboda irin ayyuka masu kyau da ya yi a jihar Legas lokacin yana gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164