2023: Idan PDP Ta Karbi Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Sake Kwana da Yunwa, Okowa

2023: Idan PDP Ta Karbi Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Sake Kwana da Yunwa, Okowa

  • Gwamnan jihar Delta ya ce da zaran PDP ta ɗare kan madafun iko ba za'a sake samun ɗan Najeriyan da zai kwana da yunwa ba
  • Ifeanyi Okowa, ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar PDP yace APC ta lalata komai a Najeriya
  • Ya roki 'yan Najeriya su zabi Atiku don kawo karshen yunwa, talauci da rashin tsaro a ƙasa

Delta - Dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya roki 'yan Najeriya su kaɗa wa Atiku Abubakar kuri'unsu da sauran 'yan takarar PDP a 2023.

Gwamna Okowa yace haka ne kadai zai tabbatar da cikar burin mutane na ganin an fatattaki yunwa, talauci da rashin tsaron da suka wa kasar nan katutu.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
2023: Idan PDP Ta Karbi Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Sake Kwana da Yunwa, Okowa Hoto: Dr. Ifeanyi Okowa
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Okowa ya yi wannan rokon ne ranar Alhamis a wurin kamfen PDP da ya gudana a kananan hukumomin Oshimili ta arewa da ta kudu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

Yace gwamnatin jam'iyyar APC da ke mulki yanzu haka ta maida hannun agogo baya na tsawon shekaru da wannan mulkin na ta na kama karya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Okowa yace gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta lalata duk wani tsarin jin dadi da walwala ciki harda bangaren ilimi, wanda ta bari malaman jami'o'i suka shiga yaji tsawon watanni Takwas.

A cewarsa, saboda Allah ya tsaga da rabon shi zai zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, ya shiga tikitin PDP a 2023, to ya gama wa al'umma aikin, kamar yadda PM News ta rahoto.

"Idan muka aje batun PDP ta bamu tikitin mataimaki wanda bamu taba gani ba tun da aka kafa jihar Delta, akwai bukatar mu zage dantse don ba maraɗa kunya kan yardar da aka nuna mana."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

"A 2019, Delta ce ta fi kowace jiha baiwa PDP kuri'u a kudu-kudu, yanzu an bamu tikitin mataimaki don haka ya rataya a kanmu mu nunka kuri'un baya saboda APC ta barnata komai a Najeriya, yunwa, rashin tsaro da rashin haɗin kai."
"APC bata san inda ta dosa ba, haushi take ji muna tallafawa mata da matasa domin su gina sana'o'i su dogara da kansu. Idan Allah ya ba ka iko ya kamata ka yi jagoranci da manufa, shiyasa Atiku-Okowa zasu tsamo ku daga yunwa."

- Ifeanyi Okowa.

APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'un Jihata Ba Zan Iya Shiga Caca, Gwamnan Edo

A wani labarin kuma Gwamna Obaseki yace ya shirye yake ya sa Cacar kudi kan cewa APC ba zata tabuka komai ba a zaben 2023

Gwamna Godwin Obaseki yace ko rantsuwa ya yi ba zai kaffara ba mutane sun gaji da mulkin APC, ba zasu sake zabenta ba a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

Ya ce yana da yakinin cewa jam'iyya mai mulki ba zata samu akalla kaso 25 cikin 100 na kuri'un jiharsa ba kuma Atiku ne zai lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262