Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Gamu da Kalubale a Takarar Shugabancin Najeriya
- Jam’iyyar APC mai-mulki tun 2015 za tayi kokarin cigaba da mulkin Najeriya bayan zabe mai zuwa
- Amma akwai cikas da Asiwaju Bola Tinubu zai ci karo da su a takararsa tun daga cikin jam’iyyarsa
- Dauko Musulmi da Tinubu ya yi a maimakon ya nemo Kirista, ya hada shi fada da wasu Kiristoci
A wani rahoto da aka fitar, Daily Trust ta jero abubuwan da za su yi tasiri a yakin neman zaben tsohon Gwamnan jihar Legas a Fubrairun 2023.
1. Tikitin Musulmi-Musulmi
Shakka babu akwai kiristocin da za su yi korafi saboda Bola Tinubu ya dauko Kashim Shettima wanda Musulmi ne a matsayin abokin takararsa a APC.
A dalilin wannan Babachir David Lawal da Yakubu Dogara suka yi watsi da takarar Tinubu.
2. Kwamitin yakin zabe
Tun daga wajen fitar da kwamitin yakin neman takara, aka samu matsala. Wasu manya a APC sun zargi Hon. James Faleke da yin watsi da su a tafiyar Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An yi mamakin rashin ganin sunayen irinsu Yemi Osinbajo, Boss Mustapha da wasu manya a jerin.
3. Karfa-karfa a zaben shugabanni
Ana zargin APC tayi wa masu neman shugabancin jam’iyya karfi da yaji wajen janye takararsu. Sai dai har yau ba a maida masu kudin da suka kashe na fam ba.
A haka Tanko Al-Makura; George Akume; Abdulaziz Yari; Sani Musa; Etsu Muhammed da Saliu Mustapha suka hakura, suka janyewa Abdullahi Adamu.
4. Zaben tsaida gwani takara
Jaridar ta na zargin akwai burbushin rashin jituwa tun wajen shiga neman takarar shugaban kasa a APC. Akwai abokan gaban Bola Tinubu da ba su huce ba.
Tinubu ya yi galaba ne a kan Rochas Okorocha, Ben Ayade, David Umahi, Ahmed Yarima, Ahmed Lawan, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, da su Yahaya Bello.
Inda matsalolin Tinubu su ke
A baya, mun kawo maku rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya na fuskantar wasu barazana wajen cinma dadadden burinsa na mulkin kasa.
Matsalar abokin takara, rashin tabbas a kan dukiyarsa da takardun shaidan ilmi da zargin rashin lafiya sun dabaibaye takarar da Tinubu yake yi a inuwar APC.
Asali: Legit.ng