Jiga-Jigan PDP da Wasu Manyan Jam'iyyu Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Oyo
- Jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya daga jiga-jigan jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyu a jihar Oyo
- Sakataren watsa labarai na APC reshen jihar Oyo, a wata sanarwa yace wannan baban nakasu ne ga manyan jam'iyyun siyasa a jihar
- Manyan jigan-jigan sun samu halartar wurin taron karban masu sauya shekar a babban filin wata makarantar Firamare a garin Oyo
Oyo - Daruruwan mambobin Peoples Democratic Party (PDP), African Democratic Congress (ADC) da kuma Accord Party sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Oyo.
Jaridar PM News ta rahoto cewa an yi wa masu sauya shekar wankan shiga APC ne a filin makarantar Firamaren Methodist da ke Apaara, a garin Oyo.
A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na APC ta jihar Oyo, Olawale Sadare, ya fitar yace sauya shekar babban koma baya ne da jam'iyya mai mulki PDP da wasu jam'iyyu.
Ya ce wannan ci gaban babbar alama ce da ke nuna shirin APC na lallasa 'yan takarar jam'iyyun dake hamayya da ita a babban zaben 2023 mai zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi a wurin taron, Azeez, tsohon jigon PDP ya ayyana tsohuwar jam'iyyarsa da koramar 'yan yaudara wacce babu ɗan siyasar da zai so gina tarihi a ciki.
Daga cikin jiga-jigan da suka sauya shekar har da, Alhaja Ejide Saka (ADC), Misis Olawumi Kola (PDP), Nurudeen Abule (AP), Misis Olaide Akande (ADP), Fasto Sulola Taiwo (Accord), Misis Eniola Oyelere (Accord) da kuma Mustapha Sakiru.
Sun samu tarba mai kyau hannu bibbiyu daga ɗan takarar Sanatan Oyo ta tsakiya a inuwar APC, Dakta Yunus Akintunde, dan takarar mambam majalisar wakilai a mazabar Afijio/Atiba/Oyo East/Oyo West, Prince Akeem Adeyemi da sauransu.
Dan takarar gwamnan Oyo na APC, Sanata Teslim Folarin, ya samu wakilci daga Yemi Aderibigbe, mataimakin daraktan kamfen APC a Oyo da Sakataren jam'iya, Tajudeen Olanite.
An halaka mamban PDP a Oyo
A wani labarin kuma Wasu Tsageru Sun Je Har Gida Sun Halaka Mamban Jam'iyar PDP a jihar Oyo
Ɗan siyasan ya rasa rayuwarsa ne a hannun tawagar 'yan daban da suke adawa da juna ranar Laraba 28 ga watan Disamba, 2022.
Jam'iyar PDP reshen jihar Oyo ta yi Allah wadai da lamarin inda ta koka cewa tana zargin harin ya samu goyon bayan wasu daidaikun mutane a tsagin 'yan adawa.
Asali: Legit.ng