Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

  • Ana ganin nasarar Atiku Abubakar a jihohi da-dama da suka ratsa kasar nan a zaben shugaban kasa
  • Watakila Atiku da Bola Tinubu na jam’iyyar APC ba za su samu akalla 25% da ake bukata a Jihohi 25 ba
  • Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun tsuke kan su sosai a yankin Kudu maso gabas da Arewa maso yamma

Abuja - Babu mamaki a zagayen farko a rasa wanda ya yi nasara a tsakanin masu neman kujerar shugabancin Najeriya a zaben shekarar badi.

Hasashen da This Day ta gudanar, ya nuna cewa ba abin mamaki ba ne sai zaben shugabancin kasa ya kai ga zagaye na biyu tsakanin masu takara.

Akwai jihohi 21 da ake kyautata zaton Atiku Abubakar mai takara a jam’iyyar PDP zai samu akalla 25% da doka tayi tanadi a zaben shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Fadawa Manoma Katon Kuskuren da Za Ayi Idan Aka Zabi Atiku

A gefe guda, ‘dan takaran jam’iyyar APC, Bola Tinubu zai iya tashi da 25% na kuri’u ne a jihohi 20.

LP da NNPP za su bayan PDP da APC

Mr. Peter Obi na jam’iyyar LP ake hangen zai zo na uku a zaben, shi kuma Rabiu Musa Kwankwaso mai takara a jam'iyyar NNPP zai kare a na hudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta fitar da sakamakon hasashen da aka yi a kowane yanki da kowace jihar kasar nan. Hakan ya nuna inda kowace jam’iyya take da karfi.

'Yan PDP
Yakin neman zaben PDP a Uyo Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Yadda ake tunanin 2023 za ta kasance

A Arewa maso tsakiya, PDP za tayi galaba a Neja, Kogi da Kwara, sai LP ta samu nasara a Filato da Benuwai, sai kuma APC ta karbe Nasarawa.

Jam’iyyar APC ake ganin za ta ci Kaduna da yayin da PDP za ta iya nasara a Jigawa, Katsina da Sokoto. Jam’iyyar NNPP kuma za ta karbe Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Peter Obi da LP ake ganin za su tashi da 60% zuwa 70% na kuri’un Enugu, Ebonyi, Imo, Abia da Anambra. Da kyar sauran jam’iyyu za su tsira a yankin.

Ana ba Bola Tinubu nasara a Legas, Ogun, Ondo, Ekiti, Oyo da Osun. PDP za ta zo na biyu da 20% a kusan duka jihohin Kudu maso yamma illa Osun.

A Arewa maso gabas, an ba APC Borno da Yobe, sai PDP ta lashe 60% na kuri’un Adamawa da rinjaye a sauran jihohin, NNPP za ta ci 5% zuwa 20%.

A Kudu maso kudu, PDP za ta iya cin Delta, Akwa Ibom da Bayelsa. LP za ta sha gaban kowa a Ribas da Kuros Riba inda Bola Tinubu zai tashi da 25%.

Shari'ar kungiya da Tinubu

An ji labari Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International tana shari’a da APC, INEC da Bola Tinubu kan zaben shugaban kasa

Kara karanta wannan

Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

Kungiyar tana neman haramtawa Bola Tinubu takarar kujerar shugabancin Najeriya, amma Lauyan ‘Dan takaran APC a zaben na 2023 yana so a janye shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng