Fitaccen Sanatan PDP Ya Ce Bola Tinubu Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023
- Magoya bayan Bola Tinubu a kudu maso gabashin Najeriya suna kara kaimi wurin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasar na APC
- Fitacce daga cikinsu shine jigon jam'iyyar PDP kuma sana daga jihar Enugu, Chimaroke Nnamani
- Nnamani ya yi gwamna a jihar Enugu daga 1999 zuwa 2007, lokaci guda da Tinubu ya ke gwamna a Legas
Agbani - Tsohon gwamnan jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani ya jadada cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ke son ya zama shugaban Najeriya na gaba.
Nnamani wanda ke wakiltar mazabar Enugu-East a majalisar dattawa, ya jadada cewa Bola Tinubu za a zaba shugaban kasar Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu mambobin kwamitin kamfen din shugaban kasa na Asiwaju, wadanda suka ziyarci garinsa na Agbani a karamar hukumar Nkanu West suma suna da ra'ayi irin nasa.
Mambobin sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani, Kakakin PCC na APC a kudu maso gabas, Josef Onoh; Onyemuche Nnamani da A.C. Udeh.
Nnamani ya fadawa bakinsa cewa yana da kyau mutane su sani cewa ba don bukatar kansa ya ke goyon bayan Tinubu ba sai don cigaban kasar Ibo a siyasar Najeriya.
Kalamansa:
"Ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, za a zabi Asiwaju Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya. Akwai bukatar mutane su sani don cigaban siyasar Ibo a Najeriya na ke goyon bayansa ba don kaina ba."
Allah ya yi wa jagoran kamfen din dan takarar gwamnan APC na Jihar Taraba rasuwa
A wani rahoton kun ji cewa mai kula da yakin neman zabe na dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Taraba, a karamar hukumar Karim Lamido ya mutu.
Hon. Abdullahi Kanti ya rasu ne sakamakon wata mummunan hadarin mota da ta ritsa da shi a Lau Road a hanyarsa na zuwa Jalingo babban birnin jihar Taraba.
Sanata Emmanuel Bwacha, dan takarar gwamna na APC a Taraba ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen dan siyasa mai son zaman lafiya, yayin addu'ar Allah ya jikansa da rahama.
Asali: Legit.ng